Leadership News Hausa:
2025-04-07@13:01:31 GMT

Hanyoyin Warware Matsalolin Ma’aurata(1)

Published: 6th, April 2025 GMT

Hanyoyin Warware Matsalolin Ma’aurata(1)

Ganduje Ya Nada Tsohon Kwamishinansa Garba, Shugaban Ma’aikatan Jam’iyyar APC  Kamshin Jiki Da Cikar Hankalin Manzon Allah (SAW)

Maimakon mu guje wa matsalolin da muke fuskanta, ya kamata mu nemi shawarar magance su. Idan kuka bi ka’idodin hakan zai taimaka muku ku magance matsalolinku.

Ku tattauna matsala:

Akwai lokacin magana, Ku tabbata cewa kun tattauna matsalar sosai.

Ka gaya wa matarka ainihin abin da ke zuciyarka da kuma ra’ayinka a kan batun. A kowane lokaci, ku gaya wa junanku gaskiya, ko da abin vacin rai ya faru kada ku yi fada. Idan ka yi maganar da za ta sanyaya zuciyar matarka ba za ku yi gardama ba.

Ko da ba ku jitu a kan wannan batu ba ku ci gaba da yi wa juna alheri da kyakkyawan zato, kada ku manta cewa ya kamata ku rika nuna wa juna kauna da ban girma, ku yi kokari ku sasanta matsalar da ke tsakaninku nan da nan, kuma kada ku ki yin magana da juna.

Shawara:

Ku keve lokaci don tattauna matsalar da ke tsakaninku, idan matarka tana magana, ka yi kokari ka kyale ta ta gama magana, idan ta gama, sai ka yi magana, ku saurara kuma ku fahimta

Ku kaunaci juna wajen ba da girma, kowa ya riga ba dan’uwansa.

Yana da muhimmanci ka kasa kunne da kyau sa’ad da matarka take magana, ka yi kokari ka fahimci ra’ayinta kuma ka yi hakan da juyayi da kuma tawali’u. Kada ka yi kamar kana saurara kawai, idan da hali ka bar abin da kake yi gabaki daya don ka saurari matarka sosai ko kuma ka tambaye ta ko za ku iya tattauna batun a wani lokaci. Idan kuka dauki juna a matsayin abokai maimakon abokan gaba, ba za ku yi garajen yin fushi ba.

Ko da abin da matarka take fada yana ci maka rai, ka ci gaba da saurarawa don ka fahimce ta ka mai da hankali ga abin da take nufi maimakon kalmomin da take furtawa. Ka lura da muryarta da kuma fuskarta yayin da take magana.

A cikin dukan aiki akwai riba, amma tadin baki ba ya nufa ko ina sai wajen tsiya, yanke shawara mai kyau kawai ba shi ne aikin ba. Kuna bukatar ku yi abin da kuka shawarta za ku yi, yin hakan ba zai kasance da sauki ba, amma za ku samu sakamako mai kyau. Idan kuka ba juna hadin kai, za ku girbi ‘amfanin wahalarku.

Kowannenku ya Kudura yin abin da zai iya yi don ku warware matsalar da ke tsakaninku a lokaci-lokaci, ku zauna ku bincika don ku ga ko kuna samun ci gaba a wannan batun.

Idan kai da matarka kuka yi kokari sosai, aurenku zai yi dadi maimakon daci. Kada ku ta da maganar da ta riga ta mutu, ku mai da hankali ga na gaba, idan kuka ba wa juna hadin kai kuma kuka bi ka’ida za ku iya warware duk wata matsala da ta kunno kai.Ka tambayi kanka.

Wace matsala ce nake bukatar tattaunawa da matata cikin gaggawa?

Me zai taimaka mini in fahimci ra’ayin matata a kan wannan batun?

To daga nan kun san abin da ya kamata ku yi, sai ku dau himma.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Ma aurata

এছাড়াও পড়ুন:

An sake kona Kur’ani mai tsarki a kasar Netherlands

Edwin Wagensfeld, mai tsattsauran ra’ayi mai tsattsauran ra’ayi kuma mai magana da yawun kungiyar Pegida ta kasar Holland, ya kona kur’ani a gaban zauren majalisa a birnin Amsterdam, a wani mataki na nuna kyama ga Musulunci, kuma wannan matakin ya haifar da fushin ‘yan siyasa da ‘yan kasar ta Holland.

A cewar gidan talabijin na Aljazeera, wannan mataki na nuna kyama ga addinin musulunci, wanda ya gudana a yammacin ranar Alhamis 4 ga watan Afrilu, ya janyo cece-kuce da suka da yawa.

Wagensfeld dai ya shahara da matsananciyar adawa da Musulunci, kuma wannan matakin ya zo daidai da kalaman nasa inda ya yi ikirarin cewa an aiwatar da wannan aiki (kona kur’ani) ne sakamakon karin matsin lamba da aka fuskanta sakamakon kona tutar Isra’ila.

Ya sanar a cikin wani sako a kan hanyar sadarwa ta X cewa: “Bayan nuna adawa da gurbatacciyar akidar Musulunci a birnin Arnhem, lokaci ne na Amsterdam.” Duk wanda ya yi tunani kadan zai gane cewa matsin lamba bayan kona tutar Isra’ila ya yi yawa sosai har aka kai ga kona Al-Qur’ani a inda muke so.

Shugaban masu tsatsauran ra’ayi ya jaddada cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba kan ‘yancin fadin albarkacin bakinsa, ya kuma yi ikirarin cewa kungiyar Pegida (mai adawa da Musulunci) za ta ci gaba da fafutukar tabbatar da kasar Netherland daga gurbatattun akidu.

Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce daga ‘yan siyasa da ‘yan kasar ta Holland, inda dan majalisar dokokin kasar ta Holland Ismail Abbasi ya bayyana lamarin a matsayin “zamantakewa ga kiyayya” tare da jaddada cewa kona kur’ani wani hari ne kan mutunci da martabar mutane sama da biliyan guda.

Ita ma ‘yar jaridar Holand Annette de Graaf ta soki abin da Wagensfeld ya yi, inda ta bayyana su a matsayin matsorata, ta kara da cewa ya kamata karamar hukumar Amsterdam ta dauki nauyin gudanar da wannan aiki.

‘Yar jaridar ta yi kira ga magajin garin Amsterdam Femke Halsema da ya ba da cikakkun amsoshi game da lamarin, domin a baya ta yi Allah wadai da kona tutar Isra’ila.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Wagensfeld ya aikata na kyamar Musulunci ba, kuma a baya ya bayyana cewa ya shirya gudanar da zanga-zanga a birnin Arnhem a ranar 20 ga watan Maris gabanin shari’ar tasa mai taken “Musulunci bai fi ‘yan Nazi ba.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An sake kona Kur’ani mai tsarki a kasar Netherlands
  • Ɓarawo ya haɗiye ɗan kunnen Naira biliyan ɗaya
  • Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — Fulani
  • Ana Ci Gaba Da Kai Ruwa Rana Takanin Amurka Da China Kan Batun Harajin Fito
  • Burtaniya Ta Soki Gwamnatin Netanyahu Kan Hana ‘Yan Majalisarta Biyu Shiga Cikin Isra’ila
  • Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya (2)
  • Kofin Duniya: Kocin Nijeriya Na Fatan Matashin Ɗan Wasan Arsenal Nwaneri Ya Wakilci Ƙasar
  • Bude Kofa Da Hadin Gwiwa Da Juna Kalmomi Ne Mafi Dadi
  • Al-Houthi: Hare-haren Amurka sun kasa dakatar da gwagwarmayar Yeman