Arzikin Nijeriya Ya Habaka Zuwa Naira Tiriliyan 22.61 A Zangon Karshe Na 2024 – CBN
Published: 6th, April 2025 GMT
Babban bankin kasar ya lura da cewa wannan raguwar ya samo asali ne sakamakon faduwar farashin danyen mai na Bonny Light na Nijeriya, wanda ya fadi zuwa dala 75.66 kan kowacce ganga daga dala 82.23 a zango na uku na shekarar 2024.
Bugu da kari, karin fitar da danyen mai daga ganga 1.33 kowace rana zuwa 1.
A gabaki-daya, sashin mai ya taimaka da kaso 00.7 cikin 100 na ci gaban tattalin arziki cikin gida (GDP) a tsawon wannan lokacin.
“Vangaren da ba na mai ba wanda ya samu tagomashi, ya samu saurin havaka da kaso 3.69 idan aka kwatanta da na zango na uku na 2024.
“Kuma wannan vangaren a gabaki-daya ya taimaka da kaso 3.77 na dukkanin ci gaban tattalin arziki, inda ya kasance sashin farko da ya jagoranci hadadar tattalin arzikin Nijeriya.
“Muhimman vangarorin da suka taka rawa wajen samun wannan ci gaba sun hada da sashin hada-hadar kudade da na inshora, vangaren sadarwa, sufuri, adana, amfanin gona da kuma vangaren kasuwanci.
“Vangaren kudade da inshora, musamman, sun samu ci gaba mai yawa saboda havaka fasahar kudi, ingantacciyar hanyar shiga banki, da karin zuba jari a kasuwanni,” in ji rahoton CBN.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Gano An Biya Wasu Ma’aikatan Bogi Naira Miliyoyi
Gwamnatin Jihar Kano ta gano matsaloli a cikin tsarin albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi, inda aka gano ma’aikata 247 da suka yi ritaya ko kuma sun mutu, amma suna ci gaba da karɓar albashi.
Wannan bayani ya fito ne daga cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Musa Muhammad, ya fitar. A cewar sanarwar, wannan bincike ya gudana ne a yayin da ake gudanar da aikin tantancewa domin gyara tsarin albashin ma’aikatan gwamnati a jihar.
Har Yanzu Da Akwai Jihohin Da Malaman Makaranta Ke Karbar Albashin Naira 18,000 NLC Ta Yi Zanga-Zanga A Ofishin Wike, Ta Nemi A Biya Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Albashin N70,000Sanarwar ta bayyana cewa, duk da cewa waɗannan ma’aikatan sun yi ritaya ko kuma sun mutu, sun kasance suna cikin jerin sunayen ma’aikatan da ke karɓar albashi, wanda hakan ya kai ga biyan kuɗi na ƙarya har Naira miliyan 27,824,395.40 a watan Maris na shekarar 2025 kawai.
Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa an dawo da wannan kuɗi zuwa asusun ƙananan hukumomi, kuma za a ci gaba da bincike don gano duk wanda ya yi wannan zamba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp