Sojoji sun kashe ’yan bindiga a Taraba
Published: 6th, April 2025 GMT
Dakarun Soji Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai.
Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa.
Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — FulaniA cewarsa, da sojoji suka isa yankin Chibi, sai ’yan bindigar suka fara tserewa.
Amma sojojin sun bi sahunsu, suka yi musayar wuta da su, har suka kashe uku daga cikinsu, sannan suka lalata maɓoyarsu tare da ƙwato makamai masu hatsarin gaske.
Sanarwar ta kuma ce sojojin sun daɗe suna sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle, inda suka tarwatsa sansanonin wasu ƙarin ’yan bindiga a baya-bayan nan.
Rundunar ta ce tana ci gaba da aiki tuƙuru domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda a faɗin Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Maɓoya Najeriya Taraba
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas ta ce a shirye take ta sako dukkan fursunonin Isra’ila da suka rage, domin musanya fursunoni”
Wani babban jami’in Hamas ya ce kungiyar a shirye take ta sako dukkan fursunonin Isra’ila da suka rage a zirin Gaza da aka yi wa kawanya, domin musanya abin da ya bayyana da ” fursunoni” da kuma tabbatar da kawo karshen yakin kisan kare dangi da ake ci gaba da yi.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto Taher al-Nunu na cewa: “A shirye muke mu sako dukkan ‘yan Isra’ila da ake tsare da su a yarjejeniyar musayar fursunoni, da kawo karshen yakin, da janyewar sojojin Isra’ila daga zirin Gaza da shigar da kayan agajin jin kai.”
A halin yanzu Hamas na tattaunawa a birnin Alkahira tare da masu shiga tsakani na Masar da Qatar.
Saidai, duk da haka, jami’in na Hamas ya caccaki Isra’ila saboda hana ci gaban da aka samu wajen tsagaita wuta.
A wani labarin kuma Akwai rahotannin da ke cewa Washington za ta yi matsin lamba kan gwamnatin Tel Aviv ta amince da wata sabuwar shawara kan tsagaita wuta a Gaza.
A ranar 18 ga watan Maris ne sojojin kasar Isra’ila suka kaddamar da wani harin ba-zata a zirin Gaza, inda suka kashe daruruwan mutane, tare da jikkata wasu da dama, tare da wargaza yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu, da yarjejeniyar musayar fursunoni.
A cewar ma’aikatar lafiya a Gaza, akalla Falasdinawa 50,983 aka kashe, akasari mata da kananan yara, tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.