Aminiya:
2025-04-07@14:05:48 GMT

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba

Published: 6th, April 2025 GMT

Dakarun Soji  Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai.

Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa.

Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — Fulani

A cewarsa, da sojoji suka isa yankin Chibi, sai ’yan bindigar suka fara tserewa.

Amma sojojin sun bi sahunsu, suka yi musayar wuta da su, har suka kashe uku daga cikinsu, sannan suka lalata maɓoyarsu tare da ƙwato makamai masu hatsarin gaske.

Sanarwar ta kuma ce sojojin sun daɗe suna sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle, inda suka tarwatsa sansanonin wasu ƙarin ’yan bindiga a baya-bayan nan.

Rundunar ta ce tana ci gaba da aiki tuƙuru domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda a faɗin Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Maɓoya Najeriya Taraba

এছাড়াও পড়ুন:

An kai wa motar haya hari an kashe mutum 2 da sace wasu a Benuwe

Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan wata motar bas ta sufurin fasinja ta Benue Links da ke kan hanyarta a titin Ikobi na ƙaramar hukumar Otukpo a Jihar Benuwe, inda suka kashe direban da wani fasinja na gaba, yayin da suka yi awon gaba da wasu fasinjojin.

Lamarin ya afku ne da yammacin ranar Alhamis a kusa da rusasshen kamfanin Benue Burnt Bricks, wanda aka fi sani da hanyar shiga garin Otukpo.

’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi Motar fasinja ta kama wuta wasu sun tsallake rijiya da baya

Motar mallakar gwamnatin Jihar ta kamfanin Benue Links Nigeria Limited tana kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo lokacin da aka yi mata kwanton ɓauna.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na kamfanin, Johnson Ehi Daniel ya fitar a ranar Juma’a, ya tabbatar da faruwar harin, ya kuma yaba da yadda jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa, tare da bayyana ƙwarin gwiwar ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da fasinjojin da aka sace.

“Benue Links Nigeria Limited ta yi takaicin sanar da harin da aka kai kan wata motar safa mai lamba PP512. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025, kusa da Otukpo Burnt Bricks lokacin da wasu mahara ɗauke da makamai suka yi wa motar kwanton ɓauna.

“Abin takaici, maharan sun harbe direban motar bas mai kujeru 18, Mista Samuel Agege da wani fasinja na gaba, yayin da ’yan bindigar suka yi yunƙurin sace sauran fasinjojin, wasu mutane uku sun yi nasarar tserewa, wani kuma ya sauka tun da farko a garin Taraku kafin faruwar lamarin,” in ji sanarwar.

Hukumomin kamfanin sufurin sun jajantawa iyalan waɗanda suka rasu tare da yin alƙawarin ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin ganin an dawo da fasinjojin da aka sace.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi
  • Gaza : adadin ‘yan jaridar da aka kashe ya haura 210
  • Harin Filato: An kashe Mutane 40, An Kona Gidaje 383, Fiye Da Mutane 1,000 An Raba Su Da Muhallansu 
  • Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno
  • An kai wa motar haya hari an kashe mutum 2 da sace wasu a Benuwe
  • An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe
  • An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu a Kudu
  • Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52