Hamas Ta Yaba Da Ma’aikaciyar Kamfanin Microsoft Wacce Ta Fallasa Yadda Kamfanin Yake Taimakawa HKI

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yabawa ma’aikaciyar kamfanin kayakin lantarki da kuma sadawar ta Microsof mai suna Ibtihal Abussad wacce ta fallasa kamfanin a bikin cika shekaru 50 da kafa shi, a dai dai lokacinda daractan kamfanin mai kula da sashen AI kirkirerren fasaha Mustafa Sulaiman yake jawabi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa Abussad ta tilastawa daraktan yanke maganarsa, inda ta fara cewa abun kunya ne kamfanin Microsuft yana taimakawa HKI da fasahar Ai ko kirkirerren fasaha a kissan kiyashin da take yi a gaza. Ta kuma fallasa yadda manya manyan kamfanonin sadanarwan da kuma kayakin lantarki suke da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza.

Daga karshen kungiyar Hamas ta bukaci sauran masana irin Ibtihal su koyi jarunta wajenta su kuma fallasa wadanda suka tabbatar da suna da hannu a yakin gaza.

Ya zuwa yanzu dai HKI ta kashe falasdinawa kimani 50,700 tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Mamaya Sun Yi Kasan Kiyashi A Zirin Gaza Da Kuma Ci Gaba Da Killace Falasdina  Cikin Masifar Yunwa

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kashe-kashen kisan kiyashi, kuma ana ci gaba da fama da yunwa a Gaza a daidai lokacin da kasashen duniya suka yi shiru

An shiga rana ta arba’in da fara sabon farmakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun ta’adi da kisan kare dangi da ba a taba ganin irinsa ba, a daidai lokacin da Amurka ke goyon bayan ta’asar da kuma shiru na kasa da kasa wanda masu lura da al’amura suka bayyana a matsayin babban abin kunya.

A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, adadin wadanda suka yi shahada  sakamakon hare-haren ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya kai 51,355 da kuma jikkatan wasu 117,248 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023.

Adadin wadanda suka yi shahada da jikkata tun daga ranar 18 ga watan Maris na wannan shekara ta 2025, watau kwanaki arba’in, ya kai kimanin shahidai 2,000 da kuma jikkatan 5,207.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Daidaikun Kasashe Za Su Kara Karfi Idan Suka Hada Hannu Tare
  • Samarin Arewa sun yaba wa Sarkin Daura kan bai wa Ja’o’ji muƙami
  • Samarin Arewa sun yaba wa Sarkin Daura kan bai wa Ja’o’ji muƙami
  • Falasdinawa 39 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’o’I 24
  • Iran Tace Ta Gamsu Da Yadda Tattaunawarta Da Amurka Yake Tafiya Zuwa Yanzu
  • Hamas Ta Yi Allawadai Da Dage Rigar Kariya Na Ma’aikatar Hukumar UNRWA
  • Sojojin Mamaya Sun Yi Kasan Kiyashi A Zirin Gaza Da Kuma Ci Gaba Da Killace Falasdina  Cikin Masifar Yunwa
  • Gaza: Falasdinawa Da Dama Sun Yi Shahada A  Yau Asabar
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
  • Duniyarmu A Yau: Shiri Kasashen Yamma Na Kashe Dukkan Falasdinwa A Gaza