Nazarin CGTN: An Bukaci Kasa Da Kasa Su Bijirewa Cin Zali Daga Amurka
Published: 6th, April 2025 GMT
Nemi adalci maimakon babakere. Cin zali ta hanyar kakaba haraji da Amurka ke yi, ya haifar da suka da adawa da martani daga kasashe da dama. Takarda mai dauke da matsayar kasar Sin da aka fitar dangane da cin zalin ta samu goyon bayan daga kasa da kasa. Sakamakon wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin masu amfani da intanet a fadin duniya, ya nuna wadanda suka amsa nazarin na kira ga kasashen duniya su hada hannu su dauki mataki domin bijirewa salon cin zali irin na Amurka, su kare hakkokinsu da kuma tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya.
Bisa fakewa da daidaito da adalci, Amurka na son cin riba daga faduwar wasu, inda take sanya muradunta sama da na al’ummar duniya. Kasar Sin na adawa da hakan tana mai bayyana neman ci gaba a matsayin ‘yanci na bai daya na dukkan kasashe ba na wasu ‘yan tsiraru ba.
Game da hakan, kaso 86.9 na masu bayar da amsa sun yi ammana cewa, matakan martani da kasashe suka dauka game da matakan Amurka na cin zali ta hanyar haraji, abu ne da ya halatta na kare muradunsu. Har ila yau, kaso 89.2 sun yi kira ga karin kasashe su dauki karin matakai na kandagarki game da batutuwan cinikayya da Amurka, suna masu bayyana adawa da yadda Amurka ke yin gaban kanta wajen cin zali a dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kamar hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO). (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
China Za Ta Kara Harajin Fito Da Kashi 34% Kan Kayayyakin Da Take Shigo Da Su Daga Amurka
Kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, ta shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka na kakaba harajin kwastam kan abokan cinikayyarta.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta ce, harajin kwastam da Amurka ta kakaba, ya matukar take halaltattun hakkoki da muradun kasashe mambobin WTO, kuma ya matukar dagula ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da kuma tsarin tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa. Bugu da kari, hukumar harajin kwastam ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, kasar Sin za ta kara sanya harajin fito na kaso 34% kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, farawa daga ranar 10 ga watan Afrilun nan da muke ciki.