JMI Ta Kaddamarda Sabbin Ci Gaban Da Ta Samu Da Fasahar Nukliya A Ranar Makamashin Nukliya Ta Kasar
Published: 6th, April 2025 GMT
Gwamnatin Kasar Iran ta bada sanarwan samun sabbin ci gaba a fagen fasaha da kuma kayakin da suka shafi makamashin Nukliya, wanda za’a baje kolinsa a ranar 9 ga watan Afrilu na wannan shekarar , wato ranar makamashin Nukliya ta kasa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto mataimakin shugaban kasa kuma shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Mohammad Eslami yana fadar haka a yau Lahadi.
Ranar makamashin Nukliya ta kasa a nan JMI dai, ita ce ranar da hukumar makamashin nukliya ta kasa take bayyana irin nasarori da kuma ci gaban da ta samu a fasahar nukliya da kuma kaddamar da abubuwan da ta samu tare da amfani da wannan fasahar a ko wace shekara. Ya zuwa yanzu dai JMI ta samar da abubuwa da sama wadanda ta yi amfani da sinadarin Uranium ko makamashin nukliya kimani 100 a cikin kasar. Wanda ya nuna irin ci gaban da ta samu, ta kuma samu a wannan fagen
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukliya ta kasa makamashin Nukliya ta kasa
এছাড়াও পড়ুন:
Muna Farin Ciki Da Karramawar Da Gwamna Abba Ke Samu Saboda Aiki Tukuru – Hon. Ibrahim
Hon. Ibrahim ya yi nuni da cewa a karkashin jagorancin Gwamna Abba an samu ci gaba sosai wajen tabbatar da samar da ingantaccen ilimi ga kowa da kowa da kyautata harkar lafiya da sufuri da biyan ma’aikata da ‘yan fansho hakkokinsu ba tare da jinkiri ba.
Kwamishinan ya jaddada goyon bayansa ga irin ayyukan raya kasa da Gwamna Abba ke yi, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, bunkasa matasa da bunkasa harkar kasuwanci da sufuri a fadin Jiha Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp