Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Southampton ba za ta buga gasar Firimiya Lig na badi ba, bayan da su ka koma gasar yan dagaji ta kasar Ingila, Southampton ta yi rashin nasara a hannun Tottenham Hotspur wanda kuma shi ne ya yi sanadiyar da Southampton ta koma gasar Championship ta kasar Ingila.

Hakan ya sa ta kasance kungiya ta farko a tarihin gasar da ta koma baya (relegation) bayan buga wasanni 31 kacal, Southampton ta samu maki 10 a wasanni 31 an zura mata kwallaye 74 a raga sannan kuma ta zura kwallaye 23 kacal a bana.

Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar Nijeriya Manchester United Na Son Lashe Firimiya A Shekarar 2028

Ramsdale tsohon mai tsaron ragar Arsenal, ya taka rawar gani a wasan inda ya tare kwallayen da ka iya shiga raga har sau biyar a wasan, ciki har da kwallayen da Spence da Dominic Solanke su ka buga cikin kwarewa da zafin nama, amma kuma bakin sun rasa damarsu a lokacin da Tel ya ci wani bugun daga kai sai mai tsaron raga, biyo bayan keta da Welington ya yi a kan Johnson.

Bayar da damarmakin da Southampton ta yi wani abu ne da ya ci mata tuwo a kwarya, hakan ya sa ta zama kulob din da aka fi zurawa kwallo a raga inda aka zura mata kwallo 74 a wasanni 31 da su ka buga, kuma abu ne da za su magance idan har su na son dawowa gasar Firimiya a kakar wasa mai zuwa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Firimiyar Ingila

এছাড়াও পড়ুন:

Zulum Ya Taya MNJTF Da Gwamnatin Alihini Bayan Harin Boko Haram A Wulgo

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƴansanda Sun Damke Ango Da Abokansa Bayan Mutuwar Amarya A Jigawa
  • Liverpool Sun Zama Zakaran Gasar Premier Bayan Lallasa Tottenham
  • Kasashen Duniya Sun Yi Ta AiIka Tallafi Bayan Fashewar Bandar Abbas
  • ‘Yansanda Sun Ƙwato Bindigogi Da Tabar Wiwi A Zamfara Bayan Artabu Da ‘Yan Bindiga
  • An gano tsohuwar da ake nema a cikin maciji
  • Bayan Shekaru 10 Madrid Da Barcelona Zasu Sake Yaɗuwa A Wasan Ƙarshe Na Copa Del Rey 
  • Shin Manchester United Za Ta Iya Lashe Kofin Europa League?
  • An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi
  • Zulum Ya Taya MNJTF Da Gwamnatin Alihini Bayan Harin Boko Haram A Wulgo
  • Kudaden Da Ke Hannun Mutane Sun Ragu Zuwa Naira Tiriliyan 5 – Rahoto