Shugaban Hukumar IAEA Ya Ce JMI Bata Da Makaman Nukliya
Published: 6th, April 2025 GMT
Rafael Grossi shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya (IAEA) ya bayyana cewa JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana dukkan kayan aikin da ake bukata, da kuma fasahar kera makamin idan tana bukatar yin hakan.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Grossi yana fadar haka a wata hira da yayi da tashar talabijin ta Agentina a yan kwanakin da suka gabata.
Abinda tambaya a nan itace tunda hukumar ta tabbatar da cewa a halin yanzu Iran bata da makaman Nukliya me yasa Amurka take tada hankali kuma take barazana ga kasar dangane da shirin ta na makamashin Nukliya al-hali bata da shi?
Grossi ya bayyana cewa al-amuran siyasa da kuma takurawa kasar da kasashen yamma suke yi shi ne yake ruruta rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da kasashen yamma. Shugaban ya tabbatar da cewa gwamnatin JMI tana bada hadin kai ga masu binciken hukumar wadanda suke gudanar da bincike a dukkan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar ta Iran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas Ta Yi Allawadai Da Dage Rigar Kariya Na Ma’aikatar Hukumar UNRWA
Kungiyar Hamas a Gaza, ta yi allawadai da ma’aikatar sharia ta kasar Amurka wacce ta cire rigar kariya ga ma’aikatan hukumar bada agaji ta falasdinwa wanda MDD take kula da ita.
Kungiyar UNRWA ta na bada agaji ga falasdinawa ne tun bayan kafa HKI da kuma korar Falasdinawa a karon farko daga kasarsu a shekara 1947.
Gwamnatin kasar Amurka ta dade tana ganin an dade ba’a wargaza hukumar ba.
Kungiyar ta kara da cewa wannan matakin ya nuna irin nuna son kai ga HKI wanda Amurka ta dade taba yi. Kuma ta bukaci kasar Amurka ta yi sauri ta maiha wannan rigar kariyar ga wadannan ma’aikata.