Leadership News Hausa:
2025-04-07@14:19:56 GMT

Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci

Published: 7th, April 2025 GMT

Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci

Game da matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya”, kasar Sin ta gabatar da jerin matakai don mayar da martani, da kuma bayyana ra’ayin gwamnatin kasar na kin amincewa da sabon tsarin haraji na kasar Amurka. Cikin bayanin da Sin ta fitar a ranar 5 ga wannan wata, ta yi nuni da cewa, kasar Amurka ta yi amfani da haraji a matsayin makamin matsawa sauran kasashe lamba da neman samun moriya ita kadai, wanda mataki ne da aka dauka bisa ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya da cin zarafin tattalin arziki, kuma Sin ta jaddada cewa, ba ta jin tsoron tinkarar wannan batu, kuma za ta ci gaba da aiwatar da manufofin cinikayya masu inganci da zuba jari cikin ‘yanci da sauki, ta yadda za ta more damar samun bunkasuwa da moriyar juna tare da kasa da kasa a duniya.

Ta wannan bayani, ana iya gano ra’ayin Sin na kin amincewa da kama karya da neman tabbatar da adalci. Farfesa a kwalejin ilmin harkokin diplomasiyya na kasar Sin Li Haidong ya bayyana cewa, wannan bayani ya shaida cewa, kasar Sin ba ta tsoron ra’ayin kama karya, kuma tana son a tabbatar da adalci, da taimakawa kasa da kasa wajen yin hadin gwiwa da kokari tare don sa kaimi ga raya tattalin arziki bisa tsarin bai daya a duk duniya. Hakazalika kuma, kasar Sin ta ci gaba da sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje, da kara imanin sauran kasashe na kin amincewa da ra’ayin kama karya, da ba da tabbaci ga yanayin duniya dake canjawa.

Ya kamata a bi ka’idoji da adalci a fadin duniya. Samun bunkasuwa ‘yanci ne na dukkan kasashen duniya, ba na wasu kasashe kadai ba. Kasar Amurka ta kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokan cinikayya daga bangare daya, lamarin da ya sabawa ka’idojin dake shafar kasashen da aka fi ba su gatanci na WTO, da sabawa odar tattalin arziki da cinikayya ta duniya. Amurka tana son zama gaban komai kuma ta musamman, kana tana son kwace ‘yancin sauran kasashen duniya na samun ci gaba. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Manyan Cibiyoyin Kudi Na Duniya Sun Yi Gargadai Akan Sabbin Kudaden Fito Na Amurka

Kungiyar kasuwanci ta duniya  ( WTO) da asusun bayar da lamuni           ( IMF) sun yi gargadi akan sakamakon dake tattare da Karin kudaden fito na kasuwanci da gwamnatin shugaban kasar Amurka Donald Trump ta yi a jiya Alhamis.

 Kungiyar kasuwancin ta duniya, ta yi hasashen cewa ci gaban harkokin kasuwanci a duniya zai sami koma baya da kaso 1% a cikin 2025, wanda hakan yake nufin akasin yadda aka yi hasashe tun da fari.

Babbar daraktar kungiyar kasuwancin ta duniya Ngoz Okonjo-Iweala ta yi gargadin cewa, Karin kudaden fito da aka yi zai iya jefa duniya cikin yakin kasuwanci,  idan kuwa kasashe su ka dauki matakin mayar da martani, to za a sami tsaiko a cikin harkokin kasuwanci a duniya.

Shi kuwa asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ta bakin shugabarsa Kristalina Ivanova Georgieva, ya bayyana cewa; Wadannan matakan da aka dauka za  jawo hatsari mai girma wajen ci gaban da tattalin arzikin duniya yake yi, musamman ma a wannan lokacin da dama ake fama da tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin na duniya yake yi.

A gobe Asabar ne dai sabon harajin na Amurka zai fara aiki, wanda ya fara daga Karin 10% akan kayan da ake shigar da su Amurka, zuwa fiye da haka gwargwadon yadda ake da gibi a tsakanin kowace kasa da Amurkan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An sayar da kare mafi tsada a duniya
  • Fedpoly Bauchi Ta Sanya Na’urorin Ɗaukan Hoto ‘CCTV’ Don Daƙile Satar Jarabawa Da Inganta Tsaro
  • Nazarin CGTN: An Bukaci Kasa Da Kasa Su Bijirewa Cin Zali Daga Amurka
  • Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya
  • Gwamnatin Kasar Sin Ta Caccaki Matakin Kakaba Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Da Amurka Ta Dauka, Ta Kuma Sha Alwashin Kare Moriyarta
  • Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Amurka Da Jakadan Sin A Burtaniya Sun Nuna Adawa Da Matakin Harajin Fito Na Ramuwar Gayya Da Amurka Ta Dauka
  • Al-Azhar ta yi kira da a kama Netanyahu a matsayin mai laifin yaki
  • Manyan Cibiyoyin Kudi Na Duniya Sun Yi Gargadai Akan Sabbin Kudaden Fito Na Amurka
  • Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Matakan Harajin Fito Na Amurka Sun Sa Ta Zama Makiyiyar Duniya