Aminiya:
2025-04-07@14:15:18 GMT

’Yan sanda sun janye gayyatar da suka yi wa Sanusi II kan hawan sallah

Published: 7th, April 2025 GMT

Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah.

Maimaikon ya Sarkin ya je Abuja domin yi masa tambayoyi, Sufeto Janar ya umarci rundunar ’yan sandan jihar, yi wa Sanusi II tambayoyi.

Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren Filato, sun nemi a yi adalci Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba

Kakakin ’yan sanda na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi ne, ya bayyana hakan, inda ya ce an soke gayyatar ne bayan da wasu manyan mutane a ƙasar suka shiga lamarin.

Ya ƙara da cewa ’yan sanda na son kauce wa duk wani da zai danganta lamarin da siyasa ko wani abu daban.

Idan ba a manta ba hedikwatar ’yan sanda ta ƙasa ce, ta gayyaci Sarkin, domin ya bayar da bayani game da wani abin da ya faru a lokacin bikin Sallah a Kano.

Tun da farko, rundunar ’yan sandan jihar, ta dakatar da duk wasu hawan Sallah da suka haɗa da jerin gwanon dawakai, saboda matsalar tsaro.

Amma a ranar 30 ga watan Maris, yayin da Sarkin ke tafiya zuwa filin Idi na Ƙofar Mata domin Sallar Idi, an kashe wani jami’in sa-kai da ke tsaronsa ta hanyar caka masa wuƙa, sannan wasu kuma sun jikkata.

Bayan haka, wasu majiya sun ce Sufeto Janar na ’yan sanda, Kayode Egbetokun, ne, ya umarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya kama Sanusi II.

Sai dai Kwamishinan ya shaida masa cewa abin da ya faru bai shafi karya dokar hana hawan Sallah ba, kuma Sarkin bai hau doki ba wajen ziyarar gidan gwamnati kamar yadda ake yi a da.

Sai dai duk haka Sufeton ya umarci sashen leƙen asiri na ’yan sanda da su gayyaci Sarkin zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hawan Sallah Sufeto Janar Na Yan Sanda Tambayoyi

এছাড়াও পড়ুন:

Duk Da Matsin Tattalin Arziki, Bukukuwan Sallar Bana Ta Yi Armashi

Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano Rano LGA:

Alhamdulillah mun yi bikin sallah lafiya kalau a garin Rano kamar yadda muka saba duk shekara kowa yana uzurinsa kamar yadda aka saba lafiya. Alhamdulillah an yi ziyarce-ziyarce lafiya gidajen ‘yan’uwa da surukai da abokan arziki da kuma haduwa da tsofaffin dalibai. Gaskiya sai godiya duba da yadda ake cikin tsadar rayuwa da wani irin hali na kuncin rayuwa a wannan a kasa ta mu sai dai mu a yankinmu na karamar hukumar Rano muna cikin alhinin kisan gillar da aka yi wa ‘yan’uwanmu a yankin kudu a jihar Edo ba zamu tava manta wannan aika-aika da aka yi mana ba Allah ya isar mana, Allah ya sa mudace Allah yasa mun yi ibadu karvabbu Allah ya maimaita mana masu amfani.

Sunana Zainab Zeey Ilyas Jihar Kaduna:

Bikin sallah ya kayatar da mu sosai sai dai wasu ba kamar yadda suka saba duk shekara ba, musamman yadda sallar ta zo ba tare da wasu sun kammala shiri ba. Na ziyarci ‘yan’uwa na na kusa da na nesa kamar Babbar Yayata, Kawu na, Aunty na, dan har garin Kano mun ziyarta, sai wuraren shakatawa, gidajen tarihi, da kuma gidan Sarki. Sallar bana za a ce da ita ma sha Allah Alhamdulillahi, an yi ta cikin zaman lafiyya da kwanciyyar hakali, mun yi kallon hawa.

Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:

Alhamdullilah Ma sha Allah, hakika mun gudanar da bikin sallar idi da shagulgulan bikin sallah cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, al’umma sun yi hidimar sallah daidai gwargwado duk da halin da ake ciki na matsin tattalin arzikin da tsadar rayuwa, fatan mu Allah ya karvi ibadar mu bakidaya. To maganar zuwa ziyara hakika mun ziyarci gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki an gaisa an yi zumunci sosai kai har ma mun samu damar zuwa garuruwan ‘yan’uwa dake nesa domin sada zumunci. To batun sallah sai mu ce Alhamdullilah Ma sha Allah tunda mun samu damar gudanar da sallah cikin nutsuwa da kwanciyar hankali domin koda ba a samu damar yin hidima mai yawa ba tunda aka samu damar gudanarwa cikin lumana dole mu godewa Allah daya ba mu wannan dama, daga karshe nake kara addu’ar Allah ya karvi ibadar mu ya yafe mana kura-kuran mu don darajar fiyayyen halitta manzon Allah (S.A.W).

Sunana Hafsat Yusuf Karamar Hukumar Isa A Jihar Sokoto:

Hidimar wannan sallar ta zamo mai kayatarwa a garin mu duk da matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin, mun kai ziyara ga ‘yan’uwa kuma mun hadu da wadanda muka dade ba mu hadu da su ba, abun akwai burgewa. Daga karshe ba abun da zan ce sai Alhamdulillah Allah ya maimaita mana.

Sunana Yasar Saleh Zareku Miga A Jihar Jigawa:

Yadda bikin sallah yake kasancewa a garin mu sai mu ce Alhamdullilah Ma sha Allah. Da zarar gari ya waye kowa da kowa zai fita filin idi dan gabatar da sallah da an sakko za ai ta kai ziyara zuwa gidan ‘yan’uwa da abokan arziki; yayye, kanne da ‘yan’uwa da abokan arziki. To sai godiyar Allah amma kam ta zo wa mutane da yanayi na tsadar rayuwa da matsin tattalin arzikin da muke fama da shi amma duk da haka Alhamdullilah tun da mun samu damar gudanar da bikin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Sunana Fatima Ibrahim Jihar Katsina:

Bikin sallah dai a unguwar da nake ya kasance abu ne mai ban sha’awa, mun je gurare da dama kamar gidan zoo, gurin wasa, gidan ‘yan’uwa da abokan arziki da gidan makama. A gaskiya dai wannan sallar za a iya cewa ta zo kwatsan dan wadansu basu tanadi dinkin sallah ba da kuma lalle da sauransu, ni dai na samu nayi da wuri komai kalau a wajena.

Sunana Fatima Nura Kila, A jihar Jigawa:

Alhamdulillah mun yi sallah lafiya inda kowa yake cikin farin ciki a wannnan rana ta sallah duk da yanayin da ake ciki, amma mutane sun yi ado daidai wadaitar kowa, fatanmu Allah ya nuna mana wata sallar. Alhamdulillah mun yi ziyarar ‘yan’uwa da abokan arziki mutanan da aka dade ba a hadu ba mun kai musu ziyara Yayin da kowa yake farin ciki da ziyarar juna. Wannnan sallar sai dai mu ce Alhamdulillah domin an samu zaman lafiya mun yi ta cikin nutsuwa,walwa da kaunar juna, Ubangiji ya karvi ibadunmu ya kai mu wata shekarar mai albarka ya sa muna raye.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƴansanda Sun Janye Gayyatar Sarki Sunusi, Zasu Zo Kano Da Kansu
  • ’Yan sanda sun soke gayyatar da suka yi wa Sanusi II kan hawan sallah
  • Kanwan Katsina Ya Yabi Gwamnatin Katsina Kan Farfado Da Al’adar Hawan Durbar
  • Duk Da Matsin Tattalin Arziki, Bukukuwan Sallar Bana Ta Yi Armashi
  • Yadda Kanawa suka huce takaicin rashin Hawan Sallah
  • ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi
  • ’Yansanda Sun Gayyaci Sanusi II Kan Kisan Jami’in Sa-kai Yayin Hawan Sallah A Kano
  • Yadda Musulman Nijeriya Suka Gabatar Da Bikin Ƙaramar Sallah Cikin Matsin Tattalin Arziƙi
  • Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno