Hassan Fadlallah: Amurka ke da alhakin ayyukan wuce gona da iri na Isr’aila a Lebanon
Published: 7th, April 2025 GMT
Wani mamba na kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya soki hare-haren da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila take kai wa a kudancin kasar Lebanon da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai jaddada cewa Amurka ce ke da alhakin kai hare-haren wuce gona da iri na sahyoniyawan.
A cewar Al-Mayadeen, mazauna kudancin kasar Lebanon sun binne gawawwakin shahidan Hizbullah 14 a garin Blida a wani gagarumin biki.
Hassan Fadlallah, wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Lebanon ya bayyana a yayin jawabinsa cewa: Gwamnatin Sahayoniya tana cin gajiyar raunin gwamnatin Lebanon ta yi, kuma muna bukatar matsayin da ya kunshi ayyuka na zahiri, hatta a matakin siyasa da diflomasiyya.
Ya kara da cewa: “Muna kira ga gwamnatin Lebanon da kada ta yi watsi da nauyin da ke kanta, kuma idan ta dauki matakin da ya dace, to za mu tsaya tare da ita.” Makiya suna amfani da wasu muryoyi a cikin gida da ke kira ga Isra’ila da su ci gaba da kai hari a cikin Lebanon, Waɗannan ‘yan amshin shata ne kuma za su sha kunya.
Fadlallah ya jaddada cewa: Bai kamata a ci gaba da wannan lamari a kudancin Lebanon ba, kuma Amurka ce ke da alhakin kai hare-haren wuce gona da iri na gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Wannan mamba na kungiyar Hizbullah ya jaddada cewa, babu batun tsro a cikin tafarkin da suke bi, kuma mutanen kudancin Lebanon sun nuna haka a aikace.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tashin Gobara A Tashar Jirgi Ruwa Na Shahid Raja’i Da Ke Kudancin Iran Ya Lashe Rayukan Mutane A Kudancin Iran
Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran
Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar Iran, wanda ya yi sanadiyyar jikkata daruruwan mutane a rahotonnin da ake da su a hannu har zuwa yanzu.
A cikin wani sabon rahoton da aka samu kan adadin mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’e, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ya ce: Adadin wadanda suka jikkata ya kai 516 ya zuwa yanzu.
Fashewar ta yi karfi sosai, ta yadda mazauna Bandar Abbas da Qeshm suma suka ji karar fashewar.
Daga baya an bayyana cewa lamarin ya faru ne sakamakon fashewar tankar mai a tashar ba tare da sanin wani dalili ba, kuma nan take aka aike da tawagogin ma’aikatar bada agajin gaggawa zuwa yankin.