HausaTv:
2025-04-07@15:24:55 GMT

Amurka ta kaddamar da sabbin hare-hare kan Yemen

Published: 7th, April 2025 GMT

Amurka na ci gaba da kai hare-hare kan Yemen, inda ta kai sabbin hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na kasar a baya bayan nan.

Kafar yada labaran kasar Yemen ta bayyana cewa, Amurka ta kai akalla hare-haren jiragen yaki guda uku a gundumar Bani Matar da ke lardin Sanaa.

Akalla fararen hula hudu ne suka mutu sannan wasu 25 suka jikkata, ciki har da mata 11 da yaro daya.

Hakazalika jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare guda hudu a tsibirin Kamaran da ke al-Hudaydah a yammacin kasar Yemen.

Wasu hare-hare uku na Amurka sun kai hari a lardin Hajjah da ke yammacin kasar Yemen.

Amurka da kawayenta sun zafafa kai hare-hare kan kasar Yemen bayan da ta koma yaki da Isra’ila sakamakon sabon kisan kiyashi da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza.

Galibin hare-haren da Amurka ke kaiwa kan gine-ginen fararen hula ne, lamarin da ke haddasa mace-mace da jikkata a tsakanin jama’a.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Yemen

এছাড়াও পড়ুন:

An Kaddamar Da Kwamitin Zaman Lafiya A Kananan Hukumomin Jahun Da Miga Na Jihar Jigawa

A wani muhimmin mataki na karfafa zaman lafiya da sulhu, gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da kwamitocin zaman lafiya da sulhu a kananan hukumomin Jahun da Miga.

A lokacin bikin kaddamarwar, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ya bayyana aikace-aikacen da aka dora wa kwamitocin.

Ya jaddada bukatar kwamitocin su gano musabbabin rikice-rikicen da suka addabi wasu sassan yankunan.

A cewarsa, wannan mataki yana nuna kudurin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar jihar.

Ya ce an dora wa kwamitocin nauyin tantance tasirin wadannan rikice-rikice a tsakanin iyalai daban-daban, bayar da shawarwari masu inganci, tare da sanar da gwamnati duk wani muhimmin abu da ke bukatar daukar mataki.

Malam Bala Ibrahim ya ce, daya daga cikin manyan aikace-aikacen kwamitocin shi ne wayar da kan al’umma game da muhimmancin hadin kai da zama lafiya.

Ya kara da cewa, an kuma dora musu nauyin warware rikice-rikice ta hanyar sulhu tsakanin bangarorin da ke rikici.

Shugaban Kwamitin Karamar Hukumar Miga, DC Atiku Musa, ya bayyana godiyarsa bisa nadin da aka yi masa, tare da alkawarin gudanar da aikinsa bisa gaskiya da adalci don sauke nauyin da aka dora musu.

 

Usman Muhammad Zaria 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hassan Fadlallah: Amurka ke da alhakin ayyukan wuce gona da iri na Isr’aila a Lebanon
  • JMI Ta Kaddamarda Sabbin Ci Gaban Da Ta Samu Da Fasahar Nukliya A Ranar Makamashin Nukliya Ta Kasar
  • Trump Ya Yada Hutunan Bidiyo Wadanda Suka Nuna Yadda Sojojin Amurka Suka Kashe Mutanen Yemen Wadanda Suke Bukukuwan Salla Karama
  • Al-Houthi: Hare-haren Amurka sun kasa dakatar da gwagwarmayar Yeman
  • Mutanen Algeriya sun bukaci a rufe ofishin jakadancin Amurka a kasarsu
  • An Kaddamar Da Kwamitin Zaman Lafiya A Kananan Hukumomin Jahun Da Miga Na Jihar Jigawa
  • Manyan Cibiyoyin Kudi Na Duniya Sun Yi Gargadai Akan Sabbin Kudaden Fito Na Amurka
  • Sayyid Husi: Hare-haren Amurka Ba Za Su Yi Tasiri Akan Karfinmu Ba
  • Kasar Sin Na Nuna Damuwa Sosai Kan Harin Intanet Da Aka Kai Mata