HausaTv:
2025-04-13@08:01:23 GMT

Kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso sun kira jakadunsu daga Aljeriya

Published: 7th, April 2025 GMT

Kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina faso dake hade a kawancen Sahel na AES, sun sanar da kiran jakadunsu a Aljeriya domin tuntuba.

A wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar Mali a yammacin jiya Lahadi, kasashen uku sun sanar da kirawo jakadunsu domin tuntuba bayan da Aljeriya ta kakkabo wani jirgi marar matuki na kasar Mali a farkon wannan wata.

Aljeriya dai ta kakkabo jirgin sojojin na Mali marar matuki a cikin daren ranar 31 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu, matakin da kasashen uku sukayi tir da shi.

A cewar gwamnatin Algiers, jirgin mara matuki da ake magana a kai ya shiga cikin kasar ne, saidai sojojin Mali sun tabbatar da cewa jirgin bai shiga cikin kasar Aljeriya ba.

Lamarin, wanda ya faru mako guda da ya gabata, kaashen na AES a wata sanarwa ta bai daya sun bayyana shi a matsayin “rashin gaskiya” da kuma keta dokokin kasa da kasa.

Firaministan Mali Abdoulaye Maiga ya musanta ikirarin Aljeriya na cewa jirgin mara matuki ya shiga sararin samaniyar Aljeriya, yana mai cewa lamarin ya nuna yadda Aljeriya ke goyon bayan ta’addanci.

A matsayin mayar da martani, Mali ta gayyaci jakadan Aljeriya tare da yanke shawarar janyewa daga kawancen sojan yankin na tsawon shekaru goma sha biyar.

Bidiyon da kungiyoyin ‘yan tawaye suka fitar ya nuna tarkacen jirgin da kamfanin Baykar na Turkiyya ya kera.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kasashen China Da EU Sun Maida Martani Kudin Fito Kan Kasar Amurka

Kasashen China da Tarayyar Turai sun maida martani kan kudaden fiton da Amurka ta kara masu.

Kamfanin dillancin labaran Rauter ya bayyana cewa kasashen Turai 27 sun kara kashi 25% ga wasu zababbun kayakin kasar Amurka masu shigowa kasashen su. Wannan dais hi ne maida martani na farko wanda kasashen turan suka yi tun bayan da gwamnatin shugaba Trump ta kara kudaden fito ga kasashen duniya da dama wadanda suka hada da China da kuma kasashen turai EU.

Labarin ya kara da cewa karin kudaden fiton sun shafi motoci da karfe da kuma karfen alminium ne da suke shigo da su daga kasar ta Amurka ne.  Banda haka karin kudaden fiton sun shafi kayakin abinci wadanda suka hada da waken soya, kayan zaki, shinkafa lemun zaki,  almonds,  taba da kuma wasu ababen hawa da kuma Kannan kwalekwale.

Jimillar kayakin da abin ya shafa zai kai Uro billiyon 22.1. sai dai wannan bai kai Euro billiyon 26 wanda gwamnatin Amurka ta karawa kasashen na turai ba.

Labarin ya kammala da cewa sabon kudaden fito na kayakin Amurkan zai fara aiki a ranar talata 15 ga watan Afrilun da muke ciki, wasu kuma 16 ga watan Mayu da kuma wasu a ranar 1 ga watan Decemba karshen wannan shekara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Burkina Faso Ya Yi Fatali Da Tayin Saudiyya Na Gina Masallatai 200 A Kasarsa
  • Mutane Da Yawa Sun Jikkata Bayan Fashewar Bam A Wata Kasuwa A Ikeja
  • Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
  • NDLEA Ta Kama Wani Mutum Mai Shekaru 75 Da Laifin Safarar Muggan Kwayoyi
  • Daidaitaccen Tunanin Sin Shi Ne Dabarar Fuskantar Da “Haukar Amurka”
  • Xi Jinping Zai Ziyarci Kasashen Vietnam Da Malaysia Da Cambodia
  • Mutum Shida Sun Mutu A Hatsarin Jirgi Mai Saukar Ungulu A Amurka
  • Iran Da Armenia Suna Fara Atisayen Hadin Giwa Don Karfafa Tsaron   Kan Iyakar Kasashen Biyu
  • Kasashen China Da EU Sun Maida Martani Kudin Fito Kan Kasar Amurka
  • ECOWAS ta damu da takun-tsaka tsakanin Aljeriya da Mali