Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Published: 7th, April 2025 GMT
Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Ribas a ranar Litinin sun harba tiyagas (barkonon tsohuwa) kan masu zanga-zangar lumana don nuna adawa da abin da suka kira rashin shugabanci nagari a kasar. Masu zanga-zangar karkashin kungiyar ‘Take It Back’ sun kuma gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas da kuma yadda ‘yansandan Nijeriya ke amfani da dokar leken asiri ta yanar gizo ba ta yadda ya dace ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: masu zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙarin ’yan Najeriya za su fuskanci talauci nan da 2027 — Bankin Duniya
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa talauci a Najeriya zai ƙaru da kashi 3.6 cikin ɗari a cikin shekaru biyar masu zuwa, ciki har da shekarar zaɓe ta 2027.
Wannan hasashe yana ƙunshe ne a cikin rahoton Bankin wanda aka fitar a lokacin taron bazara na Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da ake yi a birnin Washington, D.C., a ƙasar Amurka.
Rahoton ya jaddada cewa duk da wasu nasarorin da aka samu a harkokin tattalin arziki a kwanakin baya, musamman a ɓangaren da ba na man fetur ba a cikin rubu’i na ƙarshe na shekarar 2024, matsalolin da suka shafi dogaro da albarkatun ƙasa da kuma raunin ƙasa na iya kawo cikas ga ci gaba.
A cewar Bankin Duniya, Najeriya, tare da wasu ƙasashe masu arzikin albarkatu da masu rauni a yankin kudu da Sahara, za su fuskanci ƙaruwar talauci —saɓanin ƙasashen marasa arzikin albarkatu, waɗanda ake tsammanin za su samu raguwar talauci cikin sauri.
’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin maganiRahoton ya bayyana cewa, “Ana hasashen talauci zai ƙaru da kashi 3.6 cikin ɗari tsakanin 2022 zuwa 2027a ƙasashe masu arzikin albarkatu da masu rauni—ciki har da manyan masu tattalin arziƙo kamar Najeriya da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.”
A halin da ake ciki, Sanatan da ke wakiltar Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim, ya yi kira ga ƙasashen a Afirka, Bankin Duniya, da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da su ba da fifiko ga amfani da bayanai don ci gaban Afirka.
Da yake magana a yayin taron bazara na IMF/Bankin Duniya a Washington, D.C., Amurka, Sanata Jimoh Ibrahim ya jaddada muhimmancin bayanai a ci gaban tattalin arziki da siyasa.
Ya ce, “Idan babu bayanai ba, babu wanda zai iya rage aikata laifuka yadda ya kamata ko kuma gudanar da gwamnatin da ke da nufin cimma nasarar rage talauci.”
Ya ƙara da cewa, “Bayanai kan yawan jama’a da cikakkun bayanai na mutane sun nuna cewa ya kamata ’yan ƙasa su mallaki fasfo na tantancewa domin tattara muhimman bayanai game da su wane ne su da kuma abin da suke yi.”
Sanatan ya yi gargadi ga IMF game da yin hasashe ba tare da ingantattun bayanai ba, yana mai cewa irin waɗannan hanyoyin ba su da inganci.