Ambaliya Ta Hallaka Mutum 30 A Birnin Kinshasa Na Jamhuriyar Demokradiyar Congo
Published: 7th, April 2025 GMT
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo ya kashe aƙalla mutane 30 tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa.
Ruwan saman ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgan ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa filin jirgin sama.
A gundumar Debonhomme da ke gabashin ƙasar, ruwan ya laƙume motoci da dama, lamarin da ya tilastawa wasu mazauna ƙasar yin hijira a yayin da wasu suka yi amfani da kwale-kwale kamar yadda jam’in kamfanin dillancin labaran AFP ya shaida.
Wasu daga cikin waɗanda abun ya shafa, sun maƙale a saman gidajensu bayan da ruwan ya mamaye matakalar shiga gidanjensu.
Bugu da ƙari, Ambaliyar ya haifar da cunkoson ababen hawa a birnin da ake fama da yawan zirga zirga.
Mazauna yankin da abin ya shafa sun shaidawa manema labarai cewa sun fusata bayan da gwamnati ta ƙi kawo musu agajin gaggawa.
rfi
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ambaliya
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mutum 9 kan zargin satar mutane a Taraba
Rundunar ’yan sanda a Jihar Taraba ta cafke mutane tara kan zargin satar mutane.
Haka kuma, rundunar ta gano bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu da kuma bindigogi ƙirar AK-49 guda uku da alburusai guda arba’in da biyar a hannun waɗanda aka cafke.
Dalilin faɗuwar farashin kayan abinci a kasuwannin Arewa Ƙungiyoyin da suka yi shuhura a Firimiyar IngilaKakakin rundunar ’yan sandan, ASP James Lashen ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a birnin Jalingo.
Ya bayyana sunayen ababen zargin da aka kama da suka haɗa da Shehu Ibrahim da Abdullahi Haruna da kuma Yusuf Bello.
Sauran kuma sun haɗa da Sulaiman Muhammed da Tijjani Bello da Muhammed Umar.
Kazalika, akwai kuma Adamu Ibrahim da Solomon Nathaniel da kuma Haruna Adamu.
ASP James, ya ce ’yan sanda sun sami nasarar kama waɗanda ake zargin ne bayan samu bayanan asiri dangane da ayyukansu.
Ya ce waɗanda aka kama sun shaida wa ’yan sanda cewa suna daga cikin guggun masu satar mutane a jihohin Gombe da Filato da Kaduna da Bauchi da kuma Jihar Taraba.
ASP James ya bayyana cewa ana ci gaba da faɗaɗa bincike kan ababen zargin kuma nan gaba kaɗan za a gurfanar da su a kotu.
Ya ce kwamishinan ’yan sanda, Emmanuel Bretet ya ɗauki alwashin murkushe masu aikata laifuka a Jihar Taraba domin ganin an kare rayuka da dukiyar al’umma.