Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi
Published: 7th, April 2025 GMT
Ana fargabar cewa kimanin ’yan sa-kai 13 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka kai Jihar Kebbi a jiya Lahadi.
Lamarin ya faru ne a yankin Morai na Ƙaramar Hukumar Augie — ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani.
Wani mazauni, Malam Ibrahim Augue, ya ce maharan sun kashe mutum shida ne, suka kwashe shanu, sai ’yan sa-kai suka bi su.
“A nan suka yi wa ’yan sa-kan kwanton ɓauna, suka buɗe musu wuta, inda suka kashe guda 13 daga cikinsu.”
Ƙoƙarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan sa Kai Jihar Kebbi Lakurawa
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe ’yan bindiga a Taraba
Dakarun Soji Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai.
Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa.
Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — FulaniA cewarsa, da sojoji suka isa yankin Chibi, sai ’yan bindigar suka fara tserewa.
Amma sojojin sun bi sahunsu, suka yi musayar wuta da su, har suka kashe uku daga cikinsu, sannan suka lalata maɓoyarsu tare da ƙwato makamai masu hatsarin gaske.
Sanarwar ta kuma ce sojojin sun daɗe suna sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle, inda suka tarwatsa sansanonin wasu ƙarin ’yan bindiga a baya-bayan nan.
Rundunar ta ce tana ci gaba da aiki tuƙuru domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda a faɗin Najeriya.