Jami’an ‘yansanda a gundumar Maitama da ke Abuja sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakan gaggawa kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma zargin ‘yansanda na cin zarafin al’umma a kan ikirarin dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo.

Zanga-zangar da kungiyar ‘Take-it- Back Movement’ da kungiyoyin fararen hula suka shirya a fadin kasar ya zo daidai da ranar bikin ranar ‘yansanda ta kasa a dandalin Eagle Square da ke Abuja. Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci LEADERSHIP ta tuna cewa, hukumomin ‘yansanda sun yi gargadi kan yunkurin duk wata zanga-zanga a fadin Jihohin kasar musamman ma babban birnin tarayya (FCT). Rundunar ta jaddada cewa, ranar 7 ga watan Afrilu, rana ce da gwamnatin tarayya ta ware a matsayin ranar ‘yansanda ta kasa domin murnar jajircewa da kwazon jami’ai na rundunar ‘yansandan Nijeriya. Sun yi nuni da cewa, ayyana wannan rana a matsayin ranar gudanar da zanga-zangar, akwai wata makarkashiya a ciki.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: zanga zangar

এছাড়াও পড়ুন:

An yi wa wata mata ƙarin jini sau 36

Da farko Kinjal Lathi, ta fara cire rai daga samun haihuwa da jin daɗin zama a matsayin uwa saboda cutar borin jini ta thalassemia da take fama da ita.

Dole a riƙa yi mata mata ƙarin jini duk bayan mako biyu, sannan dole ta bi wasu ƙa’idojin cin abinci da magunguna.

Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya (2) ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi

Bayan kuma cutar da take fama da ita, akwai kuma ƙalubalen ɗaukar ciki da take fama da shi.

‘’Ina ganin fuskar ’yata sai na manta da duk wata wahalar da na sha a sanadiyar ɗaukar ciki da naƙudar,” in ji Kinjal Lathi, daga yankin Ahmedabad da ke Jihar Gujarat a kasar Indiya, inda ta ƙara da cewa, “ni da mijina mun sha kuka.”

“Akwai barazana babba ga uwa da abin da ke cikinta. Amma na yanke shawarar cika burina na zama uwa,” in ji Kinjal, kamar yadda majiyar BBC ta ruwaito.

Sai dai an yi wa Kinjal ƙarin jini sau 36 lokacin da take da ciki, amma kuma ta haifi lafiyayyiyar jaririya a ranar 12 ga watan Yulin 2019.

Ko bayan haihuwar ma, sai da aka ci gaba da yi wa Kinjal mai shekara 25 ƙarin jini, inda ta ce wasu lokutan ma ana yi mata ƙarin jinin ne a yayin da take shayar da jaririyarta.

Sannan kuma wani abun farin cikin shi ne ’yarta ba ta gaji cutar ba.

Wata ƙwayar halitta ce take samun matsala, wadda ke hana cuɗanyar jini da iska domin samar da jinin da ake kira haemoglobin, wanda shi ne yake zagayawa da jini mai ɗauke da sinadarin protein a jiki.

Yaya cutar thalassemia ke shafar juna biyu?

Ba a cika masu irin wannan cuta irin Kinjal suna haihuwa lafiya ba, kamar yadda likitan yara, Anil Khatri, wanda yake cikin kwamitin kar ta kwana na yaƙi da cutar ya bayyana.

Ya ce, bai taɓa ganin haka ba sama da shekara 30 da ya yi yana aikin kula da masu cutar ba, inda ya yi jinyar masu cutar sama da guda 100.

Akwai masu cutar kusan miliyan 270 a duniya, kamar yadda ma’aikatar lafiya da walwalar iyali ta bayyana.

Akwai na’ukan cutar da dama, ciki har da wadda ake kira ‘Hemoglobin H disease’, wadda ita ma ta kasu kashi biyu, wato nau’in alpha da beta – nau’in beta (TM) ce ta fi illa.

A Indiya akwai yara kimanin 100,000 zuwa 150,000 da suke ɗauke da cutar.

Ɗaukar ciki abu ne mai wahala ga mata masu cutar, kamar yadda likitan haihuwa, Umar Khatri ya bayyana.

Idan mace na da juna biyu, jininta yana ƙaruwa, wanda hakan ya sa jikin ke buƙatar ƙarin sinadarin ‘iron’ domin tallafa wa kai iska zuwa ga jariri.

“A ƙa’ida muna kiran mata masu juna biyu ne, su zo a duba su aƙalla sau ɗaya a wata.

“Amma ita Kinjal tana zuwa ne duk kwana 15, wanda shi ne karo na farko da muka samu hakan,” in ji Khatri.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
  • HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas
  • Zanga-zangar da za mu yi babu gudu babu ja da baya — Take It Back
  • Fedpoly Bauchi Ta Sanya Na’urorin Ɗaukan Hoto ‘CCTV’ Don Daƙile Satar Jarabawa Da Inganta Tsaro
  • An yi wa wata mata ƙarin jini sau 36
  • Da Kujerar Mulki Gara Zaman Lafiyar Kano
  • ’Yansanda Sun Gayyaci Sanusi II Kan Kisan Jami’in Sa-kai Yayin Hawan Sallah A Kano
  • 2027: Tsananin Yunwa Zai Hana ‘Yan Nijeriya Sake Zaɓen Jam’iyyar APC – PDP
  • Mutanen Algeriya sun bukaci a rufe ofishin jakadancin Amurka a kasarsu