Kazalika, a cewar kungiyar, matakin takaita fitar da nau’o’in sinadaran ba zai shafi kamfanoni masu bukatarsu ba, muddin ba sa gudanar da wasu ayyuka daka iya zama illa ga tsaron kasar Sin, da ikon mulkin kan kasar, ko moriyar ci gabanta. Har ila yau, matakan ba za su haifar da cikas ga daidaito da wanzuwar tsarin gudanar da masana’antu na kasa da kasa da na rarraba hajoji zuwa sassan duniya ba.

(Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Araqchi: Babu Wata Tattaunawa Da Aka Gudanar Tsakanin Amurka Da Iran

Iran ta sake nanata matsayinta na kin shiga shawarwari kai tsaye da Amurka kan shirinta na nukiliya, maimakon haka ta bukaci a ci gaba da shawarwarin ta hanyar masu shiga tsakani.

Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya bayyana hakan, yana mai cewa babu wata tattaunawa da aka da Washington, kuma ba za a yi irin wannan tattaunawa ba sai dai ta hanyar masu shiga tsakani.

“Mun bayyana matsayinmu, muna goyon bayan bin hanyoyi na  diflomasiyya da tattaunawa, amma ta hanyar masu shiga tsakani. Tabbas, ba a gudanar da wata tattaunawa kai tsaye tsakanin Iran da Amurka ba, ” in ji Araghchi a cikin wata sanarwa da ya fitar a dandalin Telegram.

Kalaman nasa sun zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari idan ta ki amincewa da kulla wata sabuwar yarjejeniya kan shirinta na nukiliya.

Araqchi yace, Iran ba zata taba yarda da duk wani mataki na shigo-shigo ba zurfi ba, domin kuwa irin wannan ne aka yi wa kasar Libya, a lokacin da ta yi watsa da shirinta na nukiliya kuma aka ci gaba da kakaba mata takunkumai, daga karshe kuma kasashen turai da kungiyar tsaro ta NATO suka hambarar da gwamnatin kasar a lokacin mulkin Ghaddafi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Na Shirin Gaggauta Karfafa Karfinta A Bangaren Aikin Gona
  • Kasar Sin Ta Nanata Kudurinta Na Ci Gaba Da Bude Kofa Yayin Wani Taro Da Kamfanonin Amurka 
  • Araqchi: Babu Wata Tattaunawa Da Aka Gudanar Tsakanin Amurka Da Iran
  • Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci
  • Nazarin CGTN: An Bukaci Kasa Da Kasa Su Bijirewa Cin Zali Daga Amurka
  • Wani Kwararre Ya Bukaci A Rungumi Fahasar Zamani Don Bunkasa Aikin Noma A Nijeriya
  • Kofin Duniya 2026: Kasashen Da Suka Samu Tikitin Shiga Gasar Zuwa Yanzu
  • Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya
  • Gwamnatin Kasar Sin Ta Caccaki Matakin Kakaba Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Da Amurka Ta Dauka, Ta Kuma Sha Alwashin Kare Moriyarta