Arakci: Amruka Tana Mafarkin Kulla Yarjejeniya Da Iran Kwatankwanci Wacce Ta Yi Da Kasar Libya
Published: 7th, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa, Iran ba ta kin zama teburin tattaunawa, amma ba za ta zauna gaba da gaba da Amurka ba, yana mai kara da cewa; Har ya zuwa yanzu ba a yi wata tattaunawa gaba da gaba a tsakanin Iran da Amurka ba.
Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin siyasar waje na majalsar shawarar musulunci ta Iran ya gabatar da rahoto akan hali na karshe da ake ciki dangane da batun tattaunawa da Amurka.
Arakci ya kuma fadawa kwamitin cewa; Mu ma’abota diflomasiyya da tattaunawa ne, amma za mu tattauna da Amurka ne ba kai tsaye ba,kuma duk da hakan ma har yanzu ba mu bude tattaunawa ba.”
Wani daga cikin ‘yan kwamitin ya tambayi Araki akan ko Amurka tana tunanin kulla yarjejeniya da Iran irin wacce ta yi da Libya a 2003?
Arakci ya ba shi jawabi da cewa; Abu ne mai yiyuwa mafarkin da suke yi kenan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kotun Tsarin Mulki Ta Gabon Ta Tabbatar Da Nasarar Nguema A Zaben Shugaban Kasa
Koton tsarin Mulki ta kasar Gabon din ta tabbatar da nasarar da Brice Clotaire aOligui Nguema a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi.
Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Nguema ya sami kaso 94.85.% da hakan ya mayar da shi akan gaba a tsakanin dukkanin ‘yan takara.
Nguema dai tsohon janar ne wanda ya yi juyin Mulki a cikin watan Ogusta na 2023 da ya kifar da gwamnatin Ali Bongo Odnimba.
Magoya bayan Nguema sun yi bikin hukuncin da kotun ta yanke na samun nasarsa. Zaben ya kawo karshen matakin rikon kwarya bayan kifar da gwamnatin iyalan Bongo da su ka yi kusan rabin karni akan karagar Mulki.
Zababben shugaban kasar ta Gabon ya yi alkawalin sake gina cibiyoyin gwamnatin kasar da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.
Gabon dai kasa ce mai arzikin man fetur, sai dai kuma mafi yawancin mutanen kasar suna rayuwa a cikin talauci.