HKI Ta Kai Munanan Hare-hare Akan Yankin Khan-Yunus
Published: 7th, April 2025 GMT
A rana ta 21 da Isra’ila ta sake komawa yaki da al’ummar Falasdinu a Gaza, jiragen yakinta sun kai hare-hare munanan a yankin Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama, da kuma jikkata wani adadin Falaasidinawa mai yawa.
Jim kadan bayan kai wannan harin ne dai kungiyar ta mayar da martini ta hanyar harba makamai masu linzami akan matsugunin ‘yan share wuri zauna a Asqalan da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar ‘yan sahayoniya.
A gafe daya ana gudanar da yajin aiki na gama gari a yankin yammacin kogin Jordan saboda nuna kin amincewa da yadda ‘yan sahayoniya suke yi wa al’ummar Falasdinu kisan kiyashi. Kungiyoyin fararen hula ne su kirayi wannan yajin aikin, wanda ya game yankin na yammacin kogin Jordan.
A wani labarin daga Gaza, ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar da cewa da akwai mutanen da sun haura miliyan biyu da suke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Ma’aikatar ta yi wannan sanarwar ne adaidai lokacin da ake raya ranar lafiya ta duniya, tana mai kara da cewa; a kowane lokaci yanayin kiwon lafiya a zirin Gaza yana kara tabarbarewa.” Haka nan kuma ta yi gargadi akan rufe dukkanin hanyoyin shigar da abinci cikin yankin da hakan yake jefa rayuwar yara masu yawan gaske cikin hatsari.
Wani batu da hukumar kiwon lafiya ta yankin na Gaza, ta yi gargadi a kansa, shi ne yadda Isra’ila ta hana a shigar da riga-kafin shan inna cikin yakin, da hakan zai rusa kokarin da aka yin a watanni 7 a baya na fada da wannan cuta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazan Jihar Kaduna Ta Wajibta Gudanarda Binciken Lafiya Ga Maniyatan 2025
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Musulmai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa dukkan mahajjatan da suka yi rijista domin aikin Hajjin 2025 dole ne su gudanar da binciken lafiya cikin wannan mako.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Yunusa Muhammad Abdullahi, ya fitar, inda ya bayyana cewa aikin na da nufin tantance lafiyar mahajjata kafin tafiya wannan tafiya ta ibada. Binciken lafiyar ya haɗa da gwajin ciki na dole ga mata masu shirin zuwa Hajji.
Abdullahi ya bayyana cewa wannan mataki ba domin hana kowa yin Hajji ba ne, sai don tabbatar da cewa an tanadi cikakken tallafin lafiya musamman ga mahajjatan da ke fama da cututtuka kamar su ciwon sukari da hawan jini. Ya kuma ƙara da cewa za a rika ba mahajjata abinci sau biyu a rana yayin da suke a Saudiyya.
Ya jaddada cewa sai an yi gwaje-gwajen ne a asibitocin gwamnati da aka amince da su kafin a karɓa.
“Gwajin lafiya da na ciki wajibi ne. Duk wani mahajjaci da ya ƙi amsa kiran gwajin na iya rasa gurbin hajjin sa,” in ji sanarwar.
An kuma shawarci mahajjata da su karɓi katin lafiyarsu daga hannun jami’an rijista kafin su tafi zuwa asibitocin da aka ware domin gudanar da binciken.
Rel/Adamu Yusuf