Kasashen Faransa Masar Da Jordan Sun Yi Taro Akan Gaza
Published: 7th, April 2025 GMT
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin alkahira a jiya Lahadi, inda ya sami kyakkyawar tarba daga Abdulfattah al-Sisi.
Ziyarar ta shugaban kasar Faransa a Masar tana a karkashin tattaunawar da aka bude ne a yau Litinin da kasar Jordan ta kuma ita kanta mai masaukin baki akan halin da Gaza take ciki.
Yin wannan taron dai ya biyo bayan sake dawo da yaki da HKi ta yi ne a Gaza, saboda ta ki amincewa da bude shafi na biyu yarjejeniyar tsagaita wutar yaki.
A yau Litinin shugabannin kasashen na Masar da kuma Faransa sun yi tir da sake dawo da yaki da Isra’ila ta yi a zirin Gaza, haka nan kuma kin amincewa da shigar da kayan agaji a cikin yaki.
Ana sa ran cewa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron zai ziyarci yankin Arisha mai nisan kilo mita 50 daga zirin Gaza saboda ya gana da ma’aikatan agaji a suke da sansani a wurin.
Bayan kammala taron nasu, kasashen uku sun fitar da bayani na yin kira da a tsagaita wutar yakin Gaza da gaggawa, da kuma bude kafar ci gaba da aikewa da kayan agaji zuwa yankin.
Tun da fari, shugabannin kasashen Masar da Faransa sun yi taron manema labaru da su ka nuna kin amincewarsu da duk wata siyasa ta korar Falasdinawa daga kasarsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kudaden Musanyar Kasashen Waje Da Sin Ta Adana Sun Kai Fiye Da Dala Tiriliyan 3.2 A Watanni 16 A Jere
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar sun shaida cewa, ya zuwa karshen watan Maris na bana, yawan kudaden musanyar kasashen waje da Sin ta adana ya kai dala tiriliyan 3.2407, adadin da ya karu da kashi 0.42%, wato da dala biliyan 13.4 bisa na makamancin watan Fabrairu. Hakan ya sa yawan kudaden ya kai fiye da dala triliyan 3.2 a cikin watanni 16 a jere.
An kuma bayyana cewa, a watan da ya gabata, tattalin arzikin Sin ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata ba tare da tangarda ba, inda jerin manufofin da aka bullo da su bisa yanayin da ake ciki da wadanda za a dauka bisa sauye-sauyen da ake fuskanta, na ci gaba da nuna tasirinsu a kan yakini, kuma duba da ingantacciyar bunkasar da ake samu, matakan suna kara tabbatar da yawan kudaden musanyar kasashen waje da Sin ta adana a cikin yanayi mai dorewa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp