Aminiya:
2025-04-07@23:01:28 GMT

Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno

Published: 7th, April 2025 GMT

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Lahadi, ta laƙume ƙauyukan Wanori, Sarari, da Nuguri da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno.

Aminiya ta rawaito cewa gobarar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu, da kuma raba daruruwa da muhallin su.

Saudiyya ta musanta hana ’yan Nijeriya biza Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi

Lamarin dai ya tilasta mazauna ƙauyen Wanori yin ƙaura domin gujewa gobarar da ke ci gaba da yaɗuwa.

Ibtila’in da ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoton ba a gano musabbbinsa, ya ƙara dagula wa al’ummar ƙauyen lissafi, kasancewar an samu makamancin hakan a baya, ga kuma ‘yan ta’addan Boko Haram da ke tilasta su yin gudun hijira.

Duk ƙoƙarin da manema labarai suka yi domin jin ta bakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Konduga, Honarabul Abba Ali Abbari, ya ci tura, sai dai wasu mazauna garin sun ce an gano gawarwakin maza biyu, wadanda aka binne tun a ranar Lahadi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gobara

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun janye gayyatar da suka yi wa Sanusi II kan hawan sallah

Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah.

Maimaikon ya Sarkin ya je Abuja domin yi masa tambayoyi, Sufeto Janar ya umarci rundunar ’yan sandan jihar, yi wa Sanusi II tambayoyi.

Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren Filato, sun nemi a yi adalci Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba

Kakakin ’yan sanda na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi ne, ya bayyana hakan, inda ya ce an soke gayyatar ne bayan da wasu manyan mutane a ƙasar suka shiga lamarin.

Ya ƙara da cewa ’yan sanda na son kauce wa duk wani da zai danganta lamarin da siyasa ko wani abu daban.

Idan ba a manta ba hedikwatar ’yan sanda ta ƙasa ce, ta gayyaci Sarkin, domin ya bayar da bayani game da wani abin da ya faru a lokacin bikin Sallah a Kano.

Tun da farko, rundunar ’yan sandan jihar, ta dakatar da duk wasu hawan Sallah da suka haɗa da jerin gwanon dawakai, saboda matsalar tsaro.

Amma a ranar 30 ga watan Maris, yayin da Sarkin ke tafiya zuwa filin Idi na Ƙofar Mata domin Sallar Idi, an kashe wani jami’in sa-kai da ke tsaronsa ta hanyar caka masa wuƙa, sannan wasu kuma sun jikkata.

Bayan haka, wasu majiya sun ce Sufeto Janar na ’yan sanda, Kayode Egbetokun, ne, ya umarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya kama Sanusi II.

Sai dai Kwamishinan ya shaida masa cewa abin da ya faru bai shafi karya dokar hana hawan Sallah ba, kuma Sarkin bai hau doki ba wajen ziyarar gidan gwamnati kamar yadda ake yi a da.

Sai dai duk haka Sufeton ya umarci sashen leƙen asiri na ’yan sanda da su gayyaci Sarkin zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • HOTUNA: Yadda zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta gudana a wasu biranen Nijeriya
  • Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 30 a Kongo
  • Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno
  • ’Yan sanda sun janye gayyatar da suka yi wa Sanusi II kan hawan sallah
  • Rashin ɗa’a: Gwamnatin Borno ta gargaɗi masu amfani da shafukan sada zumunta
  • ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi
  • Ɗalibai za su koma makaranta ranar Lahadi da Litinin – Gwamnatin Kano
  • Ɗaliban Kano za su koma makaranta ranar Lahadi da Litinin – Gwamnati
  • Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno