HOTUNA: Yadda zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta gudana a wasu biranen Nijeriya
Published: 7th, April 2025 GMT
A wannan Litinin ɗin ce anga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal.
Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta.
A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare haƙƙin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunƙurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi
An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu ɗauke da rubutun bayyana buƙatunsu a wasu hanyoyi da ke Ikeja, babban birnin Jihar Legas.
A Jihar Ribas kuma, masu zanga-zangar sun yi dandazo a filin Isaac Boro da ke birnin Fatakwal, amma dai ’yan sanda sun riƙa harba musu barkonon tsohuwa domin daƙile manufar da suka fito ita.
Aminiya ta ruwaito Ƙungiyar ta Take It Back na cewa zanga-zangar da za gudanar a yau babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gargaɗi masu shirin zanga-zangar a ranar Litinin 7 ga watan Afrilu a faɗin ƙasar su sake tunani domin a ranar ce ‘yan sandan ƙasar suke bukukuwa domin nuna gudunmawar da suka bayar don ci-gaban Nijeriya.
Rundunar ta ce zanga-zangar tana zuwa ne a lokacin da bai dace a yi zanga-zanga a ƙasar ba.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce rundunar ba ta adawa da ‘yancin ‘yan ƙasar na taruwa da yin gangami da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba su.
Sai dai kuma sanarwar ta ce rundunar na fargaba game da burin waɗanda suka shirya yin zanga-zangar rana ɗaya da ranar da aka ware domin yaba wa irin jajircewa da sadaukar da kai na ‘yan sandan Nijeriya.
“Bisa ga ingatattun ɗabi’un da ƙasashen duniya ke bi wajen yabawa da nasarorin ‘yan sandansu, gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakin ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sandan Nijeriya,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa bikin zai samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar daga fannoni daban-daban, ciki har da sufeto janar na ‘yan sandan ƙasashen ƙetare da kuma jami’an diflomasiyya.
“Dalilin gudanar da zanga-zanga a irin wannan ranar abin dubawa ne kuma a iya cewa wani mataki ne na ɓata sunan ‘yan sandan Nijeriya da ƙasar ma baki ɗaya,” in ji sanarwar.
“Saboda haka rundunar ‘yan sandan Nijeriya tana bai wa waɗanda suka shirya wannan zanga-zangar shawarar janyeta saboda lokacin bai dace da ita ba kuma tana da manufar aikata ɓarna,” in ji Olumuyiwa.
Dalilin da za mu yi zanga-zanga — Take It BackSai dai duk da wannan gargaɗi, ƙungiyar ta Take It Back ta ce tana nan kan bakarta domin nuna adawa kan abin da ta kira mulkin kama karya da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi a ƙasar nan.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a ƙarshen mako, jagoran ƙungiyar, Juwon Sanyaolu, ta ce za su gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar domin nuna adawa da rashin shugabanci nagari da kuma daƙile ’yancin faɗar albarkacin baki.
Ga wasu hotunan yadda zanga-zangar ke gudana:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fatakwal yan sandan Nijeriya zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mutum 2 ɗauke da ƙwayar tramadol ta N150m a Kano
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama aƙalla mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, wanda suka hada da: Muntari Shu’aibu da Imrana Rabi’u.
A wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu waɗanda ake zargin ɗauke da ƙunshi guda shida na miyagun ƙwayoyin Tramadol da aka ƙiyasta kuɗinsu ya haura Dala 92,000 (kimanin Naira miliyan 150m).
Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe Gwamnan Kano ya kafa sabbin hukumomi 4Bakori ya ce, “Rundunar ’yan sandan ta gudanar da wani samame ta hanyar fasaha da bayanan sirri, ta kama waɗanda ake zargin da wannan miyagun ƙwayoyin, biyo bayan wani rahoto da aka samu.”
Ya ƙara da cewa, kama wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na magance musabbabin munanan laifuka a jihar.
Ya ci gaba da cewa, “aikin ya biyo bayan ƙoƙarin da hukumar ta yi na daƙile ayyukan ta’addanci, waɗanda a cewarsa, galibin safarar muggan ƙwayoyi ne na sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar.”
Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa an miƙa waɗanda ake zargin ga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa reshen Jihar Kano domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban ƙuliya.
“Wannan ya yi daidai da tsarin Sufeto-Janar na ‘yan sanda na aikin ‘yan sanda da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro a tsakanin ƙungiyoyin tsaro,” in ji shi.