Muhimmin jigon dabarar raya yankunan a tare shi ne, bude kofar cimma zamanantarwa da samun wadata na bai daya ga dukkan jama’a. (Fa’iza)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An sayar da kare mafi tsada a duniya

Kwanan nan wani mai kiwon karnuka a Indiya ya biya Rupee miliyan 500 — kwatankwacin Naira biliyan 8 da miliyan 949 da dubu 481 da 589 domin sayen wani karen kerkeci na jinsin karen Shephard Caucasian, wanda hakan ya sa karen ya zama mafi tsada a duniya.

Karen mai suna Cadabomb Okami, an bayar da rahoton cewa, an yi kiwon karen mafi tsadar ne a Amurka kuma S. Satish, wani mai sha’awar kiwon kare a birnin Bengaluru da ke Indiya kuma shugaban kungiyar masu kiwon karnukan Indiya ne ya saya.

NAJERIYA A YAU: Mene ne Tasirin Shirin NYSC Bayan Shekaru 50 Da Kafa Shi? ACF ta nemi Gwamnatin Tarayya ta kawo ƙarshen kisan jama’a a Filato

Ya shahara saboda tarin nau’ukan karnuka sama da 150, ciki har da wasu da ba kasafai ba ake samun su a wasu sassan duniya.

Satish ya shaida wa manema labarai a Indiya cewa, yana jin cewa farashin Rupee miliyan 500 ya dace da Cadabomb Okami saboda a zahiri yana da nau’i na daban.

Bugu da ƙari, jinsi ne mai ban sha’awa, yana dan wata takwas kacal ya riga ya kai nauyin kilo 75 kuma tsayinsa ya kai inci 30.

“Shi wani jinsin kare ne da ba kasafai ba ake samun sa kuma yana kama da kerkeci. Wannan jinsin karen ba a taba sayar da shi a duniya a baya ba,” in ji S. Satish.

“Ina kashe kudi a kan wadannan karnuka saboda ba su da yawa. Ban da haka, ina samun isassun kuɗi domin a koyaushe mutane suna sha’awar ganin su, suna daukar hoton salfi na hotuna.

“Ni da karena mun fi samun kulawa fiye da ɗan wasan kwaikwayo a wurin kallon fim! Mu duka biyun masu jan hankali ne.”

Abin sha’awa, wannan ba shi ne farkon siyayyar karen Indiyawan da mai kiwon karnukan ya saya mai tsada ba.

A bara, ya sayi wani kare jinsin ChowChow, wanda ba kasafai ake samun baye irinsa ba, wanda ake zargin yana da kamanceceniya da dabbar dawa ta ‘red panda’ a kan Dala miliyan 3.25 — kwatankwacin Naira biliyan 4 da miliyan dari 964 da dubu dari 3 da dubu 75.

Satish yana kiwon karnukansa sama da 150 a filin kadada bakwai kuma yana nuna jinsinsu a tarukan da ke faruwa a Indiya, inda ake biyan sa tsakanin Dala 3,000 kwatankwacin Naira miliyan 4 dubu dari 5 da 82 da dubu 2500.

Ya riga ya fara amfani da Okami don dawo da jarinsa, inda yake nuna shi a wasu manyan taruka da aka yi, ciki har da shirin farkon buɗe sababbin finafinai, a Karnataka.

Ya yi iƙirarin cewa, mutane suna ta yin tururuwa don ganin kare mafi tsada a duniya fiye da yadda suka saba gani a sauran karnukan nasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Na Shirin Gaggauta Karfafa Karfinta A Bangaren Aikin Gona
  • Sabon Tsarin Harajin Kwastam Na Amurka Ya Kwace ‘Yancin Sauran Kasashe
  • An sayar da kare mafi tsada a duniya
  • Fedpoly Bauchi Ta Sanya Na’urorin Ɗaukan Hoto ‘CCTV’ Don Daƙile Satar Jarabawa Da Inganta Tsaro
  • Sin Ta Gabatar Da Dabarunta Na Raya Sana’o’i Da Fasahohi Masu Kiyaye Muhalli Ga Taron WTO
  • Wani Kwararre Ya Bukaci A Rungumi Fahasar Zamani Don Bunkasa Aikin Noma A Nijeriya
  • Yau Ta Ke Manchester Dabi 
  • Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya
  • Gwamnatin Kasar Sin Ta Caccaki Matakin Kakaba Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Da Amurka Ta Dauka, Ta Kuma Sha Alwashin Kare Moriyarta