Kudaden Musanyar Kasashen Waje Da Sin Ta Adana Sun Kai Fiye Da Dala Tiriliyan 3.2 A Watanni 16 A Jere
Published: 8th, April 2025 GMT
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar sun shaida cewa, ya zuwa karshen watan Maris na bana, yawan kudaden musanyar kasashen waje da Sin ta adana ya kai dala tiriliyan 3.2407, adadin da ya karu da kashi 0.42%, wato da dala biliyan 13.4 bisa na makamancin watan Fabrairu. Hakan ya sa yawan kudaden ya kai fiye da dala triliyan 3.
An kuma bayyana cewa, a watan da ya gabata, tattalin arzikin Sin ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata ba tare da tangarda ba, inda jerin manufofin da aka bullo da su bisa yanayin da ake ciki da wadanda za a dauka bisa sauye-sauyen da ake fuskanta, na ci gaba da nuna tasirinsu a kan yakini, kuma duba da ingantacciyar bunkasar da ake samu, matakan suna kara tabbatar da yawan kudaden musanyar kasashen waje da Sin ta adana a cikin yanayi mai dorewa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Wang Yi Ya Ce Kasar Sin Za Ta Magance Cin Zarafin Da Amurka Ke Yi Ita Kadai
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da magance cin zarafin da Amurka ke yi ita kadai, ba wai kawai don kare hakki da moriyarta ba, har ma da kiyaye moriyar kasashen duniya. Ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Tajikistan Sirojiddin Muhriddin.
Ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi harajin kwastam yayin da suka hadu a birnin Almaty domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen tsakiyar Asiya da kasar Sin karo na shida.
Wang, ya nanata cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin tabbatar da gudanar da kasuwanci cikin ‘yanci, da nuna adawa da kariyar cinikayya, da kare daidaito da adalci a duniya.
Yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Uzbekistan Bakhtiyor Saidov, duk dai a wannan ranar, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashe masu ra’ayi iri daya, wajen kiyaye damawa da kowa da kowa, da kare daidaito da adalci, da kuma nuna adawa da kariyar cinikayya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp