Aminiya:
2025-04-17@16:40:04 GMT

Mahara sun yi garkuwa da fiye da mutum 50 a Katsina

Published: 8th, April 2025 GMT

Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta Jihar Katsina sun ce ’yan bindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara.

Maharan sun kuma kashe akalla mutum shida, inda suka sake kai wani hari a yankin Ƙaramar Hukumar Ɗandume ta jihar.

Rahotanni sun ce tun daga ranar Asabar maharan suka shiga yankin kuma ba su fita ba har zuwa ranar Lahadi da rana.

Malam Ya’u Ciɓauna mazaunin garin Layin Gara ne na Ƙaramar Hukumar Funtua, kuma ya ce “Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ’yan mata da matan aure da kuma ƙananan yara har 53.

“Sun kashe mutum a Layin Gara na Ƙaramar Hukumar Funtua da kuma wasu mutum biyu a garin Mai Kwama a cikin Karamar Hukumar Ɗandume,” in ji Malam Ya’u.

Shi ma maigarin Layin Gara, Mustapha Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutanensa na cikin mawuyacin hali na rashin abinci, kwatsam kuma sai ga wannan matsala ta harin ’yan bindiga.

“Gwamnati tana ji tana gani wani abin ba a yi mana. Sojoji ma yadda ake turowa mu ba mu samu gatan an turo mana su ba, ’yan sandan da suka zo sai dai suka wuce suka nufi gardawa,” in ji Mustapha Abdullahi.

Matsalar tsaron dai ta tilasta wa mutanen yankin yin hijira da ɗan sauran abubuwan da suka rage masu, kamar yadda mai garin Layin Gara ke cewa.

Hukumar ’yan sanda a jihar ta Katsina dai ta ce tana kan bincike a kai lamarin, domin haka ba za ta ce komai ba sai ta kammala.

Matsalar tsaro na ci gaba da zama ƙarfen ƙafa a Jihar Katsina, kuma yayin da al’ummar da abin ya shafa ke ƙorafi da neman hukumomi su tashi tsaye wajen ba su kariya, gwamnati da sauran jami’an tsaro na cewa suna bakin ƙoƙarinsu wajen magance matsalar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗandume

এছাড়াও পড়ুন:

Babban Daraktan Hukumar IAEA, Zai Ziyarci Iran ranar Laraba

Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya  zai ziyarci Tehran a ranar Laraba mai zuwa.

Ziyarar ta Grossi na zuwa ne gabanin sabuwar tattaunawar da za’ayi tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar mai zuwa kan batun shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya ce shugaban hukumar ta IAEA Rafael Grossi zai ziyarci Tehran a ranar Laraba.  

Gharibabadi ya bayyana cewa, babban daraktan hukumar ta IAEA, zai gana da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami.

Ya kara da cewa “ziyarar na cikin tsarin ci gaba da hulda da hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.”

Ziyarar ta shugaban hukumar ta IAEA za ta zo ne a daidai lokacin da Iran da Amurka ke shirin gudanar da tattaunawar ta biyu, wanda Oman ta shiga tsakani a ranar Asabar data gabata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yara Kimani 3,500 Ne Suka Rasa Rayukansu A Taken Medeteranin A Shekaru 10 Da Suka Gabata
  • An Kashe Mutane 7 A Yayin Da ‘Yan Ta’adda Suka Ƙaddamar Da Wani Sabon Hari A Adamawa
  • Matashi ya kai kansa ofishin ’yan sanda
  • Rasha Ta Sanar Da Kashe Manyan Kwamandojin Sojin Ukraine Fiye Da 60 A Birnin Sumy Na Kasar Ta Ukraine
  • Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 ta jikkata 69 a awa 24 a Gaza
  • Sojoji sun ceto mafiya 16 da aka yi garkuwa da wasu a Filato
  • An yi garkuwa da masu ibada a Kogi
  • Yadda kisan mutum fiye da 50 a Filato ya tayar da ƙura
  • Sojoji sun kama ’yan bindiga 12 a Nijar
  • Babban Daraktan Hukumar IAEA, Zai Ziyarci Iran ranar Laraba