Kisan Janar Alƙali: Kotu ta ɗage shari’a zuwa 28 ga Mayu
Published: 8th, April 2025 GMT
Kotu ta dage shari’ar kisan Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayu, 2025, domin waɗanda ake tuhuma su fara gabatar da shaidunsu.
Babbar kotu da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, ta ɗage shari’ar ne biyo bayan bayan ɓangaren masu ƙara su. gabatar da ga Manjo Janar U. I. Mohammed mai ritaya game da kisan.
Janar Alkali, wanda ya kasance tsohon shugaban gudanarwa a Hedikwatar Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, ya ɓace ne makwanni kaɗan bayan ya yi ritaya daga aikin soja, a lokacin da yake hanyar tafiya Bauchi daga Abuja. Mamacin ne yake tuƙa kansa a lokacin da yake tafiyar inda ya biya ta Jihar Filato.
A lokacin da ya ba ce a shekarar 2018, Janar Mohammed shi ne Kwamandan Sansanin Runduna ta 3 kuma ya jagoranci aikin neman da ceto jami’in da ya ɓata.
Mahara sun yi garkuwa da fiye da mutum 50 a Katsina NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar HannuShi ne ya jagoranci aikin da ya kai ga gano motar Janar Alkali a wani rami mai zurfi a yankin Du, daga baya kuma aka gano gawarsa a wata tsohuwar rijiya a kauyen Guchwet da ke gundumar Shen a Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.
A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan masu kare kai ya yi wa Janar Mohammed tambayoyi tare da neman ƙarin haske kan bayanan da ya bayar a baya da kuma shaidarsa dangane da mutuwar Janar Alkali.
Tambayoyin, wadanda suka dauki kimanin awanni biyu, sun mayar da hankali ne kan bayanan da ya bayar na farko da kuma waɗanda suka biyo baya game da lamarin.
Bayan zaman kotun, Mai Shari’a Arum Ashom ya sallami shaidan kuma ya tsayar da ranar sauraron karar na gaba.
Lauyan masu gabatar da ƙara, Simon Mom, wanda ya wakilci Babban Lauyan Jihar Filato, bai nuna adawa da dage shari’ar ba.
Daga bisani, alƙali ya dage shari’ar zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayu domin masu kare kai su fara gabatar da nasu bayanan kare kansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Shari a Jihar Filato
এছাড়াও পড়ুন:
Mahaifi ya yi wa ’yarsa ciki a Bauchi
’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin ya ɗirka wa ’yar cikinsa mai shekara 17 ciki a yankin Kariya da ke Ƙaramar Hukumar Ganjiwa a Jihar Bauchi.
Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya ce an kama mutumin mai shekaru 50 ne bayan samun ƙara cewa ya yi wa ’yar tasa fyaɗe fiye da sau ɗaya a ɗakinsa.
Wakil ya ce a yayin bincike magidancin ya amsa cewa ya sha zakke wa ’yar tasa a gida, kuma bayan an yi mata gwaji a asibiti aka tabbatar cewa tana ɗauke da ciki wata uku.
Ya ce yarinyar ta shaida wa masu bincike cewa a lokacin da mahaifiyarta ta yi tafiya zuwa garin iyayenta a Ƙaramar Hukumar Ningi da ke jihar ne mahaifin nata ya yi amfani da damar ya riƙa lalata da ita.
An kashe mutum kan zargin satar kare a Bauchi Darasi daga rayuwar Dakta Idris AbdulAzeez Dutsen Tanshi ’Yan bindiga sun harbi alkali da ɗansa, sun sace mutane 13 a KatsinaBayan dawowar mahaifiyar ce ta lura da alamun juna biyu a tare da ’yar, kuma bayan ta titsiye ta, ta shaida mata cewa mahaifinta ne ya yi mata cikin.
Wakil ya ce rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.