Gobara ta kona motoci 10 a garejin Borno Express
Published: 8th, April 2025 GMT
Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motocin kamfanin sufurin Borno Express na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane 18 kowacce.
Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Litinin, bayan wani fashewa mai ƙarfi a harabar garejin.
Ko da yake babu wanda ya rasa ransa a wannan lamarin, wani ma’aikacin hukumar kashe gobara ya samu raunuka yayin da yake kokarin kashe gobarar.
Wani ganau ya ce, “Gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar tukunyar gas — inda wani kara mai ban tsoro ya sa ma’aikata da matafiya a yankin suka yi ta gujegujen domin tsira.”
Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Mahara sun yi garkuwa da fiye da mutum 50 a Katsina Kisan Janar Alƙali: Kotu ta ɗage shari’a zuwa 28 ga MayuYa ƙara da cewa, “Hanzarin da hukumar kashe gobara ta yi ne ya hana lamarin ƙara ƙazancewa. Sun isa da sauri kuma sun yi nasarar shawo kan gobarar.”
Kwamishinan Sufuri da Makamashi na Jihar Borno, Aliyu Buba Bamanga, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru amma ya ƙi yin tsokaci.
Kwamishinan ya ce, “Muna jiran Mai Girma Gwamna Babagana Umara Zulum nan ba da jimawa ba. Ba zan so yin magana kafin wata sanarwa ta hukuma daga gare shi ba.”
Wani ma’aikacin garejin ya shaida wa wakilinmu cewa galibin motocin da abin ya shafa motocin bas ne masu ɗaukar mutane 18 da ake yi wa gyaran yau da kullum, da kuma wasu ƙalilan da ake yi musu manyan gyare-gyare.
“Mun auna arziki da gobarar ba ta shafi wurin cajin motocin lantarki da ke kusa ba, da gobarar ta kai can, da munin lamarin ya ɓaci.”
Garejin gyaran motocin, wanda Kamfanin Sufuri na Borno Express ke gudanarwa, yana da alhakin kula da motocin zirga-zirgar jama’a na jihar.
Wannan lamarin ya faru ne kwana daya kacal bayan wata gobara ta cinye dubban gidaje a wasu yankuna huɗu a Alau, Jihar Borno, ind ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu tare da lalata dukiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara
এছাড়াও পড়ুন:
ECOWAS ta damu da takun-tsaka tsakanin Aljeriya da Mali
Kungiyar ci gaban kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ta nuna damuwa kan takun-tsakar da ya kunno kai tsakanin kasar Mali da makwafciyarta Aljeriya, lamarin da ya kai ga kasashen biyu janye jakadu a tsakaninsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ecowas ta ce “Tana bibiyar abin da ke faruwa wanda ya shafi dangantakar da ke tsakanin kasar Mali da kuma Aljeriya.
Ecowas din ta ce ta damu matuka kan lamarin, tana kuma mai kira ga kasashen na Mali da Aljeriya da su kai zuciya nesa, su yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen warware sabanin ra’ayin da ke a tsakaninsu.”
Dangantaka tsakanin Mali da Aljeriya, ta yi tsami ne bayan da a makon da ya gabata Aljeriya ta kakkabo wani jirgi maras matuki mallakin sojojin kasar Mali, wanda ta ce ya keta iyakar kasarta.
Mali ta mayar da martani ta hanyar yi wa jakadanta da ke Aljeriya kiranye, haka nan ma kasashen kumgiyar yankin Sahel na AES, sun bi sahun Mali ta hanyar daukar irin wannan mataki, Lamarin da ya sanya ita ma Aljeriya ta mayar da martini makamancin wannan ga kasashen.