Najeriya: An gudanar da zanga-zangar adawa da wasu shirye-shiryen gwamnati
Published: 8th, April 2025 GMT
An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wada ta barke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal.
Zanga-zangar wadda wata kungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargadin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta.
A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare hakkin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunkurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi
An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu dauke da rubutun bayyana buƙatunsu a wasu hanyoyi da ke Ikeja, babban birnin Jihar Legas.
A Jihar Ribas kuma, masu zanga-zangar sun yi dandazo a filin Isaac Boro da ke birnin Fatakwal, amma dai ’yan sanda sun rika harba musu barkonon tsohuwa domin daƙile manufar da suka fito ita.
Kungiyar ta Take It Back na cewa babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gargaɗi masu shirin zanga-zangar a ranar Litinin 7 ga watan Afrilu a faɗin kasar su sake tunani domin a ranar ce ‘yan sandan kasar suke bukukuwa domin nuna gudunmawar da suka bayar don ci-gaban Nijeriya.
Rundunar ta ce zanga-zangar tana zuwa ne a lokacin da bai dace a yi zanga-zanga a kasar ba.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan kasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce rundunar ba ta adawa da ‘yancin ‘yan kasar na taruwa da yin gangami da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba su.
Sai dai kuma sanarwar ta ce rundunar na fargaba game da burin wadanda suka shirya yin zanga-zangar rana daya da ranar da aka ware domin yaba wa irin jajircewa da sadaukar da kai na ‘yan sandan Nijeriya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun laifuka, inda ta cafke wasu fitattun mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane.
Waɗanda aka kama sun haɗa da: Babaro Baushe mai kimanin shekara 40 da Umaru Dau’a, mai kimanin shekara 25 da suka fito daga ƙauyen Askuwari a ƙaramar hukumar Tarmuwa a ranar 9 ga Afrilu, 2025.
Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a KebbiA takardar sanarwar da kakakin rundunar ‘Yan sandan Yobe, SP Dungus Abdulkareem ya fitar ya ce, hedikwatar ’yan sanda reshen Dapchi da misalin ƙarfe 0500hrs, 9 ga Afrilu, 2025, ta cafke waɗanda ake zargin, ’yan ƙungiyar da suka ƙware wajen yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma neman barace-barace, suna gudanar da ayyukansu a ƙananan hukumomin Dapchi da Tarmuwa.
An dai alaƙanta waɗanda ake zargin da laifuka da dama da suka haɗa da: A ranar 21 ga Nuwamba, 2024, masu garkuwar sun kai hari ƙauyen Badegana da kuma kai hari gidan wani da aka kashe, wanda ya yi sanadin rasa rai.
A ranar 10 ga Maris, 2025, waɗanda ake zargin sun karɓe N250,000 da ƙarfi daga Mudi Ibrahim na ƙauyen Askuwari, ƙaramar hukumar Tarmuwa, bayan sun yi barazanar sace shi ko kuma su kashe shi.
Waɗannan mutane sun amsa laifukan da suka aikata, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a sashin bincike na jihar (SID).
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado ya ba da umarnin ci gaba da ƙoƙarin kama wasu ’yan ƙungiyar kuma ya buƙaci al’umma da su bayar da sahihan bayanai don taimakawa wajen gudanar da bincike.