Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Ci Gaba Da Gudanar Da Taron Bita Ga Alhazai
Published: 8th, April 2025 GMT
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ci gaba da gudanar da tarurrukan bita ga maniyyata aikin Hajjin bana, bayan kammala azumin watan Ramadan.
Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, hukumar za ta tabbatar da cewa maniyyata sun sami horo da ilimi kan yadda ake aiwatar da aikin Hajji domin dacewa wannan ibada da suka kashe makudan kudade don gannin sun aiwatar da ita.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce, za a wayar da kan alhazai da kuma koya musu yadda za su kula da kansu da kuma yadda za su aiwatar da aikin Hajji bisa ga koyarwar addini.
Ya ce, ana gudanar da wannan taron bitar ne a kullum, a cibiyoyi 27 da aka ware a fadin jihar.
Haka kuma, ya ce, taron bitar zai taimakawa Alhazan wajen fahimtar dokoki da sabbin tsare-tsaren da hukumomin Saudiyya da hukumar Hajji ta kasa NAHCON suka tsara domin aikin Hajjin shekarar 2025.
Labbo ya yi kira ga dukkanin alhazan bana da su rika halartar wadannan tarurruka domin sanin abubuwan da suka dace.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma yaba maniyyatan bisa yadda suke daukar wannan taron koyarwa da muhimmanci.
Daraktan ya kuma shawarce su da su ci gaba da nuna dabi’un kirki kamar yadda suka saba, tare da zama jakadu nagari ga jihar, da kasa baki daya, tare da bin doka da oda a masarautar Saudiyya.
Ya ce, hukumar ta riga ta tanadi masauki mai tsafta kusa da Masallacin Harami ga alhazan jihar, tare da shirya yadda za a rika ba su abinci ta hannun wani kamfani na kasar Saudiyya.
Labbo ya kuma yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da hadin kai da yake bai wa hukumar a kowane lokaci.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Taron Bita
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar Sojan Nijeriya Ta Fara Gasar Wasanni A Sakkwato
Runduna ta 8 ta sojojin Najeriya ta fara gasar wasanni ta kasa da ake gudanarwa duk shekara a jihar Sokoto da nufin karfafa sojojin Najeriya don shiryawa tsaron kasa.
Babban Jami’in Kwamandan runduna ta takwas Manjo Janar Ibikunle Ajose ya ce gasar tana nuni ne kai tsaye ga hafsan hafsoshin sojin kasar na ganin an gyara da sauya dabarun jagoranci da fagen fama a matakin farko.
GOC wanda ya samu wakilcin kwamandan runduna ta 78 da ke samar da kayayyaki da sufuri, Birgediya Janar Moses Udom Ikobah, ya bayyana cewa fafatawar ta yi daidai da kokarin da rundunar sojojin Najeriya ke yi na inganta yaki da ta’addanci ta fuskar tsaro.
Ya bukaci dukkan mahalarta taron da su kiyaye mafi girman matsayin wasanni, aiki tare, da rikon amana.
A jawabin maraba da Kwamandan, Birgediya Janar AbdulMalik Jibia Mohammed, shiyya ta 8, ya bayyana farin cikinsa da gudanar da taron tare da bayyana muhimmancinsa fiye da yadda ake gudanar da gasar.
Ya ce an shirya gasar ne domin karfafa kananan shugabanni, da karfafa kimar aikin soja, da kuma samar da kwakkwaran runduna a tsakanin sojoji da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin sassan, tare da kara kaimi, da juriya, da dabara na jami’an da ba manyan jami’ai ba.
Birgediya Janar Abdulmslik Jibia wanda ya ba da misali da dabarun da atisayen ke da su, ya ce gasar za ta kunshi abubuwa da dama da suka hada da karatun taswira, ninkaya, atisayen iri iri, da juriya, da sarrafa makamai, da nufin gwada shirye-shiryen yakar duk wani abin da zai taso.
Gidan Rediyon Najeriya dake Sokoto ya ruwaito cewa, taron wanda ya dauki tsawon mako guda ana gudanar da shi, ya tattaro tsare-tsare daga sassan sassan, da suka hada da bataliya ta 1 da 17 da 48 da 58, da kuma rundunar da aka kafa, duk sun fafata ba don daukaka ba, sai dai don nuna shirye-shiryensu na gudanar da aiki da kuma kwazonsu na kwarewa.
NASIR MALALI