Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga Algeria
Published: 8th, April 2025 GMT
Kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga kasa Algeria bayan takaddamar da ta barke tsakaninta da Mali.
Kasashen uku da ke karkashin mulkin soja sun sanar da daukar wannan matakin hadin gwiwa ne bayan Mali ta zargi sojojin Algeria da harbo wani jirginta mara matuki a sararin samaniyarta a karshen watan Maris.
A ranar 1 ga Afrilu, Algeria ta sanar cewa ta harbo wani jirgin sama mara matuki mai dauke da makamai a sararin samaniyarta, amma ba ta yi karin bayanin ba.
A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Mali ta ce hukumomi sun tabbatar da “cikakken yakini” cewa an harbo jirgin ne a cikin “A matsayin harin makiya da aka shirya daga gwamnatin Algeria.”
Gobara ta kona motoci 10 a garejin Borno Express Kisan Janar Alƙali: Kotu ta ɗage shari’a zuwa 28 ga MayuSanarwar ta ce an gano burbushin jirgin kilomita 9.5 kudu da iyakar Algeria kuma an harbo shi ne da “makami mai linzami.”
Da take bayyana shi a matsayin “abin da bai taba faruwa ba na cin zarafi,” sanarwar ta ce Mali “ta yi Allah wadai da kakkausan harshe game da wannan aikin makiya, rashin abokantaka, da kuma nuna girman kai daga hukumomin Algeria.”
Algeria ba ta yi wani tsokaci nan take game da janye jakadun ba, amma ta sanar a ranar Litinin cewa ta rufe sararin samaniyarta ga jiragen sama da ke zuwa ko tafiya Mali.
Ma’aikatar tsaron Algeria ta ce, “Saboda yawan keta hurumin sararin samaniyarmu da Mali ke yi, gwamnatin Algeria ta yanke shawarar rufe zirga-zirgar jiragen sama da ke zuwa ko tafiya Mali, tun daga yau.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jirgi mara matuki Nijar Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Ruwa Ya Ci Rayukan Mata Biyu A Kano
Mazauna karamar hukumar Gezawa ta Kano sun shiga cikin tashin hankali da makoki sakamakon nutsewar wasu mata biyu a cikin wani tafki.
Rahotanni sun nuna cewa matan (an sakaya sunansu) sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke wanka a kogi bayan sun dawo daga aiki a wata masana’antar sarrafa hibiscus.
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abdullahi Gezawa hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga ‘yan banga da ke yankin tare da bayyana cewa “Yan uwan matan biyu ne suka kai rahoton lamarin ga dan banga”
Ya yi nuni da cewa, nan take aka tura tawagar masu aikin ceto zuwa wurin, inda suka yi nasarar zakulo gawarwakin su a sume, daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu.
Saminu ya bayyana cewa an mika gawarwakin ga wani dan sanda Musa Garba na sashin ‘yan sanda na Gezawa.
Ya shawarci jama’a da su daina zuwa kusa da kogi domin gujewa abubuwan da ba a zata ba.
KHADIJAH ALIYU