Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas.
Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu.
Hundeyin ya ce makwabta ne suka kwarmata wa Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke yankin Okokomaiki, bayan mutumin ya kashe ’yar tasa ya kuma binne ta a cikin harabar gidansu.
Jami’in ya ce ““Bayan samun rahoto jami’anmu suka ce suka gano kabarin, suka tono gawar aka gudanar da bincike,” shi kuma yana hannun hukuma yana amsa tambayoyi.
Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga Algeria Kisan Janar Alƙali: Kotu ta ɗage shari’a zuwa 28 ga Mayuউৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda kashe yarsa Yarsa
এছাড়াও পড়ুন:
Macron : Faransa na shirin amincewa da yankin Falasdinawa a matsayin kasa
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya ce kasarsa na shirin amincewa da yankin Falasdinawa a matsayin kasa nan da watanni masu zuwa.
Ya ce hakan na iya faruwa a farkon watan Yuni nan wannan shekarar a taron Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a New York.
kawo yanzu, Kasashe 147 ne suka amince da yankin na Falasdinawa a matsayin kasa mai yanci.
Kasashen Sifaniya da Ireland da Norway su ne na baya-bayan nan da suka nuna amincewarsu a watan Mayun bara da yankin na Falasdinawa a matsayin kasa mai yanci, matakin da ya fusata Isra’ila.
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa da dama dai na ganin samar da kasashe guda biyu Falasdinu da Isra’ila shi ne gimshikin samar da zaman lafiya a yankin.