Sin Za Ta Mai Da Martani Kan Barazanar Kara Kakkaba Mata Harajin Kwastam Daga Amurka
Published: 8th, April 2025 GMT
Jami’in ya ce, barazanar da Amurka ke yi game da kara tsananta matakin da za ta dauka, kuskure ne dake nuna muguwar aniyarta ta dakile moriyar sauran kasashe, kuma tabbas Sin ba za ta amince ba ko kadan.
Kasar Sin ta sake nanata ra’ayinta cewa, ba wanda zai ci gajiyar tayar da zaune tsaye a goggayar ciniki, da aiwatar da manufar kariyar ciniki, don haka tana kalubalantar Amurka da ta gyara kuskurenta, tare da soke harajin da ta kakkaba mata, da daina matsa mata lamba kan tattalin arziki da ciniki, da warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar shawarwari bisa turbar mutunta juna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Allah-wadai Da Karin Harajin Amurka Ta Kuma Jaddada Goyon Bayanta Ga Ka’idojin WTO
A nata martani kuwa, Okonjo-Iweala ta ce, karuwar takun saka ta fuskar cinikayya ya haifar da babban kalubale ga tsarin bunkasar cinikayya da tattalin arzikin duniya. Don haka ta jaddada muhimmancin rungumar budadden salo na bin ka’idar cudanyar mabambantan sassa, kana ta jaddada wajibcin warware dukkanin takaddama ta hanyar tattaunawa mai ma’ana karkashin dandalin WTO. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp