Yan Sanda A Saudiya Sun Tsare Wata Bafalasdinya Saboda Bayyana Tutar Kasarta A Kan Jakarta A Masallacin Ka’aba
Published: 8th, April 2025 GMT
Jami’an yan sanda a birnin Makka sun tsare wata Bafalasdiniya wacce ta baje Jakarta dauke da tutar kasarta Falasdinu tare da zarginta na bayyana wani abu na siyasa a lokacin aikin umran da take yi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Mint-Press yana cewa matar ta shiga masallacin haramin Ka’aba dauke da jakanta mai tutar falasdinu.
Ya zuwa yanzu dai ba wanda ya san halin da take ciki. Amma ba wannan ne karon farko wanda Jami’an tsaron kasar Saudiyya suke tsare wadanda suke dauke da tutar Falasdinu a aikin hajji ko umra ba, tare da zarginsu da cewa suna hada addini da siyasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Jihar Kaduna Ta Yi Tanadin Masauki Na Musamman Ga Alhazan Bana
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta samu nasarar samo ingantaccen masauki ga alhazan jihar a birnin Makkah, gabanin gudanar da aikin Hajjin 2025.
Daya daga cikin mambobin kwamitin musamman da ke kula da aikin hukumar, Malam Buhari Marabar-Jos ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Kaduna.
Buhari Marabar-Jos ya bayyana cewa masaukan sun cika dukkan sharuddan da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya suka gindaya.
Ya kuma bayyana cewa wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, tana can ƙasar Saudiyya don kammala sauran shirye-shirye kafin dawowarsu Najeriya.
Ya jaddada cewa Gwamna Uba Sani ya ƙuduri aniyar kula da jin daɗin alhazan jihar, tare da tabbatar da cewa gwamnati ta himmatu matuƙa wajen ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi da nasara.
Ya yi kira ga maniyyata aikin Hajjin bana da su ci gaba da halartar taron bita na mako-mako da hukumar ke gudanarwa a faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Safiyah Abdulkadir