Hamas Ta Yi Allawadai Da Gwamnatin Falasdinawa Kan Masu Goyon Bayanta A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
Published: 8th, April 2025 GMT
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yi tir da gwamnatin Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, saboda dirar mikiyan da ta yi kan Falasdinawa a yankin wadanda suke zanga-zangar beman HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da ta yi a gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Litinin ce, Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, suka rufe shagudansu da harkokin kasuwancinsu da kuma ofisoshinsu don neman HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da suke yiwa yan uwansu kuma yan kasarsu a Gaza.
Majiyar kungiyar Hamas ta kara da cewa wannan dabawa kungiyar wuka a baya ne. Ta ce gwamnatin Falasdinawa a Ramallah tana wa yahudawan HKI aiki, tana taimaka mata wajen kissan falasdinawa a Gaza.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Falasdinawa a yankin
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Zamfara Ta Yaba Da Cigaban Ayyukan Tituna A Jihar
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan gina tituna da gyare-gyare a fadin jihar.
Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Alhaji Lawal Barau Bungudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar.
Alhaji Lawal Barau Bungudu ya bayyana cewa, tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal mulki, gwamnatin ta ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa, musamman gine-gine da sake gina tituna, a wani bangare na babban shirinta na sabunta birane da nufin kawo sauyi a jihar da kuma saukaka zirga-zirgar ababen hawa.
Ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen fadada hanyoyin jihar domin ingantawa da bunkasa harkokin tattalin arziki, inda ya bayyana cewa ana gudanar da ayyukan da ake gudanarwa a daidai lokacin da aka amince da su.
Alhaji Lawal Barau Bungudu ya kuma bayyana cewa, an riga an kammala ayyukan tituna da dama, yayin da wasu da dama kuma suke mataki daban-daban na kammala su.
Ya ba da tabbacin cewa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da sanya ido a kan ci gaban da aka samu don tabbatar da isar da kayayyakin aiki a kan lokaci ba tare da tsaiko ba.
Kwamishinan ya jaddada cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta mayar da hankali wajen gyara tsofaffin tituna, da suka lalace da kuma gina sabbi domin bude yankunan karkara da birane.
Alhaji Barau Bungudu ya yi nuni da cewa, ana aiwatar da dukkanin ayyukan tituna da ake yi tare da bin ka’ida mai inganci, yana mai jaddada cewa, ‘yan kwangilar an ba su aikin samar da ababen more rayuwa masu dorewa da za su tsaya tsayin daka.
Ya yi kira ga mazauna yankin da su goyi bayan kokarin gwamnati ta hanyar kiyaye ababen more rayuwa da kuma hada kai da ‘yan kwangila a yayin gudanar da ayyukan.
Kwamishinan ya nanata kudirin gwamnatin na mayar da jihar Zamfara abin koyi wajen samar da ababen more rayuwa a yankin Arewa maso Yamma.
COV/AMINU DALHATU