Hukumar Kula da Jin DDaɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ayyana ranar Juma’a 11 ga Afirilun 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana ga dukkan maniyyatan jihar.

Shugaban hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da manema labarai a Ilori.

Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa jimillar kuɗin aikin hajjin bana ya kai naira miliyan 8,459,000.

Ya yi kira ga dukkan maniyyatan da suka  fara biyan kuɗi da su tabbatar sun kammala ragowar kuɗin kafin ranar ƙarshe, wato 11 ga Afrilu, domin ba za a ƙara lokaci ba.

Alhaji Abdulsalam ya kuma buƙaci maniyyatan da su gaggauta miƙa fasfo ɗin su na tafiya ƙasashen waje ga jami’ansu domin fara aikin biza ba tare da wani jinkiri ba, yana mai jaddada cewa fasfo mai inganci da ke da aƙalla watanni shida da fara amfani ne kawai za a amince da shi.

Ya bayyana cewa miƙa fasfo da wuri na da matuƙar muhimmanci domin kauce wa jinkiri ko rikice-rikicen da ka iya tasowa wajen fitar da biza a ƙarshe.

Alhaji Abdulsalam ya shawarci maniyyatan da su kasance masu ɗabi’a tagari da yayin zamansu a kasa mai tsarki.

Ya bayyana cewa kamfanin jirgin sama na Max Air ne aka bai wa alhakin jigilar  mahajjatan Jihar Kwara na shekarar 2025 hukumance, yana mai cewa hukumar alhazan na aiki kafada da kafada da kamfanin don tabbatar da tafiyar da aikin jigilar cikin kwanciyar hankali kuma akan lokaci.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kwara

এছাড়াও পড়ুন:

Tawagogin gwamnatin Kongo da kungiyar M23 sun isa  Doha domin tattaunawa

Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na M23 sun isa Qatar domin tattaunawa don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Jami’an Kongo da masu shiga tsakani na kungiyar M23 sun isa Doha babban birnin kasar Qatar domin tattaunawa da nufin cimma tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen fadan da aka shafe watanni ana gwabzawa a yankin, kamar yadda wasu majiyoyi hudu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a jiya Alhamis.

Wakilan tawagogin biyu sun tabbatar da kasancewarsu a babban birnin kasar Qatar, kuma sun ce za a yi ganawar ido-da-ido a ranar Laraba, amma har yanzu suna tattaunawa kan tsarin tattaunawar.

Dukkanin majiyoyi – jami’an gwamnati biyu da wakilan ‘yan tawaye – sun bukaci a sakaya sunansu saboda masu shiga tsakani na Qatar sun nemi kada su yi magana da manema labarai.

Qatar ta yi wata ganawa a watan da ya gabata tsakanin shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi da takwaransa na Rwanda Paul Kagame. Wannan ita ce ganawa ta farko da shugabannin biyu suka yi tun bayan da kungiyar ta kaddamar da hari a ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata. Yunkurin yin shawarwarin zaman lafiya na baya-bayan nan shi ne yunkurin kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru ana yi, wanda ya samo asali daga kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda a shekara ta 1994.

Wata majiya da ke da masaniya kan shiga tsakani na Qatar ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa bangarorin biyu sun yi wata ganawar sirri a birnin Doha a farkon wannan wata domin shirya tattaunawar sulhu. Sai dai har yanzu tattaunawar da aka shirya fara a ranar Laraba na fuskantar cikas.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Nijeriya Na Karbo Bashin Dala Biliyan 12 Daga Kasar Japan
  • GORON JUMA’A
  • Masarautar Kauru Ta Bayyana Rashin Sha’awarta Kan Shiga Sabuwar Jihar Gurara
  • Tawagogin gwamnatin Kongo da kungiyar M23 sun isa  Doha domin tattaunawa
  • Sabon Kwamishinan Na Kwara Ya Sha Alwashin Dakile Laifuka
  • Gwamnatin Sakkwato na biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 – NLC
  • Malaman Makarantun Firamare 1,800 Sun Samu Horo Aka A Kwara
  • Za Ayi Aiki Hadin Gwiwar Tsakanin Efcc Nuj Domin Yaki Da Hako Ma’adanai A Neja
  • Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 10, Sun Kashe Ɗan Bindiga 1 A Katsina
  • Hajjin 2025: Jihar Kaduna Ta Yi Tanadin Masauki Na Musamman Ga Alhazan Bana