Li Qiang Ya Tattauna Da Shugabar Kwamitin EU
Published: 9th, April 2025 GMT
Li Qiang ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, kasar Amurka ta sanar da kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokanta na cinikayya ciki har da Sin da Turai, wanda mataki ne da bangare daya ya dauka, da ba da kariya ga cinikayya, da cin zarafin tattalin arziki. Ya ce, kasar Sin ta dauki matakai don tabbatar da ikon mulkinta da moriyar samun ci gaba cikin aminci, kana da tabbatar da ka’idojin cinikayya da adalci a duniya.
A nata bangare, Ursula von der Leyen ta bayyana cewa, matakan kara buga harajin kwastam na kasar Amurka sun kawo illa ga cinikayya tsakanin kasa da kasa, tare da yin mummunan tasiri ga kasashen Turai da Sin da sauran kasashe marasa karfi. Ta ce, bangarorin Turai da Sin sun yi kokarin tabbatar da tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban daban bisa tushen WTO da adalci da ‘yanci, da kiyaye bunkasa huldar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata, lamarin da ya dace da moriyar bangarorin biyu har ma da ta duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
E.U. ta dauki wasu sabbin matakan kalubalantar harajin fito na Amurka
Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da cewa kungiyar za ta kaddamar da matakan yaki da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya dora mata.
Kungiyar mai kasashe mambobi 27 tana fuskantar kashi 25% na harajin shigo da kayayyaki kan karafa, aluminium, da motoci, da kuma karin harajin kashi 20% akan kusan duk wasu kayayyaki karkashin manufofin Trump.
Domin mayar da martani, Tarayyar Turai za ta aiwatar da ayyuka, galibi an saita su a kashi 25%, kan nau’oin kayayyakin da ake shigo da su daga Amurka, wanda zai fara daga ranar Talata mai zuwa a matsayin martani na musamman ga harajin karafa na Amurka. Kungiyar har yanzu tana kimanta tsarinta na magance tasirin karin haraji.
Kayayyakin na Amurka da tsarin na tarayyar turai zai shafa sun hada da masara, alkama, shinkafa, injina , kaji, ‘ya’yan itace, tsirrai, tufafi, a cewar wata takarda da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya sake dubawa.
Kwamitin kwararrun masana harkokin kasuwanci daga kasashe mambobi 27 na Tarayyar Turai sun kada kuri’a kan shawarar hukumar a yammacin Laraba. Jami’an diflomasiyya sun ba da rahoton cewa mambobi 26 ne suka goyi bayan shawarar, inda Hungary kadai ta nuna adawa da hakan.