Gaza: Isra’ila ta kashe fararen hula 58 a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata
Published: 9th, April 2025 GMT
Adadin wadanda suka yi shahada a zirin Gaza ya karu zuwa 58 a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata, yayin da wasu 213 suka jikkata sakamakon kazamin harin bam da Isra’ila ta kai a yankin.
Jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da gidajensu, a ci gaba da luguden wutar da suke yia kan fararen hula a yankuna da dama na Gaza.
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da samun sabbin adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda adadin shahidai ya kai 50,810 yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 115,688.
Adadin wadanda suka raa rayukansu tun daga ranar 18 ga Maris ya kai 1,449 sannan 3,647 suka jikkata.
A cikin wannan yanayi, wakilin Al-Mayadeen ya rawaito cewa, dakarun mamaya sun kai wani gagarumin farmakin a yankunan arewacin zirin Gaza. Har ila yau sun kafa wani sansanin soji a yankin Al-Muntar da ke unguwar Shuja’iyya da ke gabashin birnin Gaza, wanda ya zo daidai da lokacin hare-haren jiragen sama a yankunan gabashin unguwar.
Akasarin wadanda suka rasa rayukansu dai mata ne da kananan yara da kuma tsoffi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Boko Haram Na Ci Gaba Da Mamaye Sassan Jihar Borno -Zulum
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp