Ibas ya naɗa kantomomin ƙananan hukumomin Ribas
Published: 9th, April 2025 GMT
Kantoman Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, ya amince da naɗin sabbin kantomomi na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Ribas, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya fitar a safiyar wannan Larabar a birnin Fatakwal.
’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Likitocin Nijeriya dubu 16 sun yi ƙaura zuwa ƙetare — Ministan LafiyaSanarwar ta ce Ibas ya kuma amince da sauya duk majalisun gudanarwa na ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin jihar da a baya aka dakatar da ayyukansu.
Sanarwar ta ce naɗin sabbin masu kula da gudanarwar ƙananan hukumomin zai fara aiki ne nan take daga ranar Litinin, 7 ga watan Afrilu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Siminalayi Fubara
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Boko Haram Na Ci Gaba Da Mamaye Sassan Jihar Borno -Zulum
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp