Sharhin Bayan Labarai: Yakin Kasuwanci Tsakanin Amurka da Kasashen Duniya
Published: 9th, April 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta.
///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fidda jadawalin kudaden fito ga dukkan kayakin da suke shigowa Amurka daga wadannan kasashen, daga ciki har da kasashen Turai da kuma kasar Chaina, ya zuwa yanzu dai kasar china ta maida martani da kashi 34% na kayakin Amurka da suke shigowa kasar China, sannan Amurka ta kara maida martani ga kasha 104 kan kayakin kasar china masu shigowa Amurka, sannan kasashen turai da dama sun ce za su maida martani.
A halin yanzu dai tasirin wannan yaki ya fara shafar kasashe da dama a duniya daga ciki har da ita kasar Amurka inda ‘kasuwannin hannun jari na kasar Amurka dai sun yi ta faduwa a ranar talatan da ta gabata da kuma ranar laraba 8-9 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2025.
Labaran da suke fituwa daga kasuwannin hannun jari na “World Treet”na kasar Amurka sun nuna cewa a karon farko tun shekarar da ta gabata, hannayen jari a kasuwar ko kasuwannin sun kai kara da 5000. Hannun jari a wannan kasuwar ya ragu da kasha 20 % daga cikin watanan fabrairun da ya gabata.
Sai dai a ranar laraba kasar China ta kara yawan kudin fito wa kayakin Amurka masu shigowa kasar zuwa kasha 84%, kuma ta bayyana cewa a shirye take ta ci gaba da wannan yakin na tattalin arziki har zuwa karshenta.
Kafafen yada labarai na kasar China sun bada sanarwan kara kodaden fito kan kayakin Amurka wadanda suke shigowa kasa har na kashi 80% sannan a shirye take ta ci gaba da yakin kasuwanci da gwamnatin shugaba Trump har zuwa karshe, inji kamfanin dillancin labaran Xinhuwa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’an gwamnatin kasar China na fadar haka a ranar Laraba sun kuma kara da cewa, idan gwamnatin Trump bata dakatar da wannan yakin kasuwanci ba to kasar China tana da hanyoyi da dama wadanda zata ci gaba da wannan yakin har zuwa karshensa.
Kafin haka dai gwamnatin shugaba Trump ta karawa kayakan kasar China masu shigowa Amurka kudaden fito daga kashe 34% zuwa kasha 104 % kuma a ranar Laraba ne, kuma dokar karin da gwamnatin kasar China ta yi zai fara aiki ne a ranar 10 ga watan Afrilu da muke ciki wato ranar Alhamis.
A ranar laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara kudaden fito ga kasashen duniya da dama daga cikin har da kasar China wacce ta maida martani bayan kwanaki biyu da kwatankwacin abinda Amurka ta kara mata.
Shugaban kasar Amurka a shafinsa na yanar gizo wanda ake kira ‘Trump Social’ ya rubuta cewa : Duk tare da gargadina na cewa duk wata kasa da ta maida martani ga kudaden fito da na dorawa kasar, to zata fuskanci karin kudaden fito daga bangaremmu, amma kasar China bata yi amfani da wannan gargadin ba ta maida martani da kasha 34% gwagwadon fiton da na dora mata.
Kakakin ma’aikatar kasuwanci na kasar China ya bayyana cewa, barazanar Amurka na kara yawan kudaden fito ga kayakin kasar China idan mun maida martani kuskure ne kan wani kuskuren don kasar China ba zata taba amincewa da hakan ba.
Manufar wannan yakin tattalin arzikin da shugaba kasar Amurka ya fara, ita ce, cire duk wani tasirin da kara kudaden fito zai yi a harkokin kasuwancin kasar ta Amurka. Sai dai ya zuwa yandai muna garin tasirin a fili.
Amurka dai ta dauki kasashen Turai da China amatsayin masu gasa da ita kuma kuma makiyanta a fagen karfin tattalin arziki a duniya.
A halin yanzu dai kasashen turai suna shirin hada kai da kasar China don tsara yadda zasu fuskanci kasar Amurka a wannan yakin tattalin arziki ko kasuwancin da suka shiga.
Dangane da wannan firai ministan kasar China ya bayyana cewa kasar China da kuma tarayyar Turai zasu tsara wani shiri wanda zai maida kasashen turai da Chaina wata babbar kasuwa a duniya don fuskantar shuagaban kasar Amurka a yakin tattalin arziki da ya fara da su a ranar 2 ga watan afrilun da muke ciki.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasashen Turai da ta maida martani tattalin arziki kasar China ta a wannan yakin kasar Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Zai Ziyarci Kasashen Vietnam Da Malaysia Da Cambodia
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatarsa da sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam kuma shugaban jamhuriyar gurguzu ta Vietnam ya yi, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai kai ziyarar aiki kasar daga ranar 14 zuwa 15 ga wata.
Haka kuma, bisa gayyatarsa da firaministan kasar Malaysia da sarkin Cambodia suka yi, shugaban na kasar Sin kuma sakatare janar na JKS, zai ziyarci kasashen Malaysia da Cambodia daga ranar 15 zuwa 18 ga wata. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp