Yadda Kasashen Afirka Za Su Iya Rage Illar Harajin Amurka
Published: 10th, April 2025 GMT
Dokar bunkasa ci gaban Afirka da samar da dama ga yankin (AGOA), wacce ta bai wa kasashen yankin damar fitar da kayayyaki zuwa Amurka ba tare da haraji ba, ta shiga gararamba bisa yadda karin harajin zai kassara masana’antu kamar su masaku, da na karafa, da kuma noma.
Nijeriya da Afirka ta Kudu da suka fi karfin tattalin arziki a yankin, Amurka ta kakaba musu haraji na kaso 14% da 30% bi-da-bi, saboda rashin imani kuma karamar kasa kamar Lesotho wacce du-du-du karfin tattalin arzikinta na GDP bai wuce dala biliyan 2 ba, aka dankara mata karin harajin da kashi 50%.
Galibin tattalin arzikin kasashen Afirka ya fi dogaro ne da fitar da kayayyaki zuwa ketare don dorewar samar da aikin yi da kudaden shiga ga gwamnatoci, to amma kuma yanzu Amurka ta zama kadangaren bakin tulu. Babu makawa kasashen Afirka su kara karkata zuwa kasar Sin da sauran kasuwanni don samun damammakin cinikayya. Kamar yadda Shugaban Ghana John Mahama ya bayyana kwanan baya, wadannan sauye-sauye da ake samu kwanan nan na iya zama alheri ga Afirka ta hanyar dogaro da kansu.
Kasashen Afirka za su iya amfani da yanayin da ake ciki wajen zurfafa alaka da Sin, wadda ta kara habaka kasuwancinta da zuba jari a duk fadin nahiyar. A maimakon kari, ita kasar Sin ta bullo da manufar cire harajin ne ma ga kasashen Afirka 33 da suka fi fama da koma bayan tattalin arziki, da ba da damar shiga kasuwanninta. Wannan ya bude sabbin damammakin ga masana’antun Afirka su fitar da kayayyakinsu zuwa kasar musamman a fannin noma.
Haka nan, kasashen Afirka za su iya yin hadin gwiwa da kasar Sin don inganta kasuwancinsu a bangaren fasahohin zamani wadda duniya ke kara karkata a kai, inda hakan zai karfafa samar da tsarin cinikayya ta intanet da bude sabbin kasuwanni masu amfani da fasaha.
Da yake yawancin kasashen Afirka sun riga sun karbi shawarar ziri daya da hanya daya na BRI, wanda ke samar da kudade don ayyukan more rayuwa, za su iya amfani da wannan ma don kara karfafa hada-hadar sufuri da kyautata huldar cinikayya da za su kara musu kwarin gogayya da sauran shiyyoyin duniya. Bugu da kari, gwamnatocin Afirka na iya karfafa ‘yan kasuwa na gida su shiga cikin hadin gwiwar da suke kullawa da Sin don karfafa masana’antu na cikin gida.
Tabbas, ta hanyar yin cudanya da kasar Sin bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni masu dacewa, kasashen Afirka za su iya rage illar kare-karen harajin Amurka, da samar da daidaiton huldar cinikayya mai tallafa wa ci gaban tattalin arzikinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasashen Afirka za su iya
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Minista Ya Zargi Isra’ila Da Kasashen Yammacin Turai Da Kitsa Kashe-kashen Rayuka A Nijeriya
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci. Hadin Gwiwar Kasashen Asiya Da Afirka Na Habaka Karfinsu Na Dogaro Da Kai Da Cin Moriya Tare Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace Tsakanin Sin Da Malaysiya “Suna shigowa su yanka mutanenmu, suna kashe Kirista da Musulmi, ’yan Arewa da ’yan Kudu,” inji shi. “Suna so su hargitsa kasar nan, kuma su bata sunan gwamnati, an taba kitsa irin hakan kuma har yanzu ana sake kitsa hakan.” Da yake zayyana makamancin haka, Fani-Kayode ya yi gargadin cewa, rikicin da ake fama da shi na da kamanceceniya da yadda aka kirkiri tashe-tashen hankula a zabukan shekarar 2015, inda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fuskanci irin wannan tashin hankali. “Haka aka shirya a shekarar 2014 kafin a kayar da Goodluck Jonathan, yanzu kuma sun fara shirin irin haka domin tunkarar 2027,” in ji shi. “Mun san su wane ne, kasashen waje daga cikin kasashen Yamma da Isra’ila da wasu da dama. Ba sa son kwanciyar hankali a Nijeriya.” Fani-Kayode ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya da su kara daukar kwararan matakai. Ya bukaci gwamnatin jihar Filato da ta kara kaimi sosai sannan ya bukaci da a kara sa ido kan iyakokin Nijeriya. Ya karkare da sakon hadin kai da juriya da kishin kasa, “Nijeriya za ta ci gaba da wanzuwa, Nijeriya ba za ta fadi ba, za mu taka matsayi kan matsayi, kuma dimokuradiyyarmu za ta dore da nufin Allah, kuma mu tsaya a dunkule wuri daya. Allah ya tsare Nijeriya.”Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp