Aminiya:
2025-04-12@21:41:27 GMT

’Yan bindiga na neman N100m kafin sakin Faston da suka sace a Kaduna

Published: 10th, April 2025 GMT

Wasu ’yan bindiga sun nemi a ba su Naira miliyan 100 kafin su sako wani fasto da suka yi garkuwa da shi a Jihar Kaduna.

Faston, mai suna Samson Ndah Ali, mai shekaru 30, yana aiki da cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke Mararaba Aboro, a Ƙaramar Hukumar Sanga.

Mutanen da suka saba ba ni abinci yanzu na neman taimako — Obi ’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna Mutfwang

An sace shi da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Litinin, lokacin da ‘yan bindigar suka shiga gidansa.

Faston ya fara aiki a cocin ne ƙasa da makonni biyu kafin wannan lamarin ya faru.

Sakataren cocin, Yusuf Ambi, ya ce yana tare da Faston a daren da lamarin ya faru.

Ya ce washegari an kira shi a waya aka sanar da shi cewa faston ya ɓace.

Da ya isa gidansa, ya tarar ƙofofin a buɗe babu kowa a ciki.

Daga bisani, maharan suka kira, suka nemi a ba su Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.

Ambi ya ce har yanzu suna tattaunawa da maharan.

Dakarun tsaro da suka haɗa da sojoji, ’yan sanda da jami’an DSS sun fara aiki tare don ceto faston.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce zai yi bayani daga bisani.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki a NUPRC — Buba Galadima

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu, ya taimaki ’yarsa ta samu aiki a Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NUPRC).

Galadima, ya bayyana haka ne yayin wani shiri a gidan talabijin na AIT.

Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur zuwa N865 Yadda masu safarar ɗan Adam ke yaudarar mutane ta intanet

Ya ce duk da yana yawan sukar gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki, har yanzu shi da Shugaba Tinubu abokai ne.

Ya ce: “Abokai ne mu kuma za mu ci gaba da zama abokai. Idan ina buƙatar wani abu daga gare shi, zan iya tambayarsa.

“Bari na faɗi gaskiya a idon duniya. ’Yata ce ta yi amfani da wayata ta kira Shugaban Ƙasa, shi kuma ya yi zaton ni ne. Sai suka ce ’ya’yana ne, suka sanar da shi al’amura sun yi tsanani.”

Ya ƙara cewa: “Sun faɗa wa Tinubu cewa ‘mahaifinmu ba zai iya wannan ba, amma ya faɗa mana kai abokinsa ne.’

“Ɗaya daga cikinsu ta ce ta kammala NYSC amma ba ta samu aiki a NUPRC wacce Gbenga Komolafe ke jagoranta.

“Tinubu ya ‘kira Komolafe, ya ce ku bai wa ’yar abokina aiki.’ Shi ya sa ta ke son zuwa Makkah don yi wa Allah da Shugaban Ƙasa godiya.”

Galadima ya kuma bayyana cewa ’yarsa ta yi aiki a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na tsawon shekara huɗu ba tare da an taɓa biyanta albashi ba.

Ya ce: “’Yata ta yi aiki da shi (Buhari) har na tsawon shekara huɗu, kuma ya bayar da umarnin kada a biya ta albashi.

“Sai dai duk wata a kawo takardar da ke nuna an biya ta. Ta yi aiki da Buhari shekara huɗu a ofishin Osinbajo ba tare da ta karɓi ko sisin kwabo ba,” in ji shi.

Galadima, ya kuma ce shi kansa ya yi aiki tare da Buhari na tsawon shekara goma sha uku.

Wannan kalamai sun bai wa mutane da dama mamaki, musamman ganin cewa Galadima ya shahara wajen sukar gwamnatin APC a fili.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina
  • An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa
  • ’Yan bindiga sun harbi alkali da ɗansa, sun sace mutane 13 a Katsina
  • Masarautar Kauru Ta Bayyana Rashin Sha’awarta Kan Shiga Sabuwar Jihar Gurara
  • ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi
  • Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki a NUPRC — Buba Galadima
  • Tarkon Mutuwa a Katsina: Hanyar Funtua zuwa Ƙanƙara
  • An Sace Dalibin Jami’ar Tarayya Birnin Kebbi
  • Mata Sun Yi Zanga-zanga Kan Yawaitar Satar Mutane A Kogi
  • Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Bayan Kashe Ɗan Bindiga A Katsina