Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Bayan Kashe Ɗan Bindiga A Katsina
Published: 10th, April 2025 GMT
An yi nasarar kashe wani ɗan bindiga yayin da jami’an tsaro suka kuɓutar da mutane 10 da aka sace a wani samame na haɗin gwiwa a karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina. Waɗanda aka ceton da suka haɗa da mata shida da maza huɗu, an yi garkuwa da su ne daga kauyukan Kiroro, Kabbi, da Dogon Marke da ke karamar hukumar ta Musawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Sace Dalibin Jami’ar Tarayya Birnin Kebbi
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ta tabbatar da sace wani dalibi dan aji 4 na Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, mai suna Augustine Madubiya, mai shekaru 23 da haihuwa, wanda ke Sashen Tattalin Arziki zuwa inda ba a san inda aka nufa ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa, wasu gungun ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki gidan Istijaba Villa da ke karamar hukumar Kalgo a jihar inda suka yi garkuwa da wani dalibi a dakin kwanan dalibai a harabar jami’ar, kuma abin bakin ciki, wani Malam Siddi Hussaini, wanda ke kusa yana kiwon shanun sa, a lokacin da yake kokarin shiga tsakani, shi ma likita ya samu rauni a harin.
A cewarsa, yayin da yake samun rahoton, jami’in ‘yan sanda na yankin, Kalgo, ya tara tawagar jami’an tsaro hadin gwiwa zuwa wurin da lamarin ya faru, kuma a halin yanzu rundunar jami’an tsaro na ci gaba da sintiri dazuzzuka da kuma hanyoyin da ke kusa da wurin da nufin ceto wanda aka yi garkuwa da shi ba tare da jin rauni ba tare da damke wadanda suka aikata wannan ta’asa.
Hakazalika, a ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne na Lakurawa da ke dauke da manyan muggan makamai suka kai farmaki kauyukan Tungan Taura da Tungan Ladan, a karamar hukumar Augie a jihar Kebbi, inda suka yi awon gaba da wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba, suka kashe mutum goma sha shida.
SP Nafiu Abubakar ya ce, tun daga lokacin an dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa kuma an fara gudanar da cikakken bincike.
Abdullahi Tukur