Ya jinjina wa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar aikin.

Gwamnati ta yaba da ƙwazon jami’an da suka halarci aikin kuma ta sha alwashin ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin jihar.

“Za mu ci gaba da fatattakar waɗanda ke barazana ga zaman lafiya a Katsina.

Za mu yi amfani da duk wata hanya da albarkatu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a,” in ji Kwamishinan.

Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa haɗin kan al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen ‘yan bindiga.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Jami an Tsaro Yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Ku Kyautata Rayuwar Jama’a Ba Kan Kanku Ba — Buhari Ga Gwamnonin APC

Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna.

Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne.

Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya da girmamawa da gudunmawar Buhari wajen gina demokradiyya da ƙarfafa jam’iyyar APC.

Uzodinma ya yaba wa Buhari saboda salon shugabancinsa, da yadda ya miƙa mulki cikin natsuwa ga wani shugaban APC, tare da aiwatar da shirye-shirye a fannonin tsaro, noma, ilimi da ababen more rayuwa.

Ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu, APC na samun kwarjini, kuma ya gode wa Buhari saboda goyon bayan da ya nuna masa a bainar jama’a.

Ya kammala da roƙon Buhari da ya ci gaba da bai wa jam’iyyar shawara da jagoranci domin ganin APC ta ci gaba da mulki da kawo wa Nijeriya ci gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina
  • Kashe-kashen Filato: Jami’an tsaro na sassauta wa masu laifi —Tsohon gwamnan soji
  • ’Yan bindiga sun harbi alkali da ɗansa, sun sace mutane 13 a Katsina
  • Jami’an Amurka da na Saudiyya sun tattauna batutuwan da suka shafi Gaza da yankin
  • Tarkon Mutuwa a Katsina: Hanyar Funtua zuwa Ƙanƙara
  • Ku Kyautata Rayuwar Jama’a Ba Taku Ba — Buhari Ga Gwamnonin APC
  • An Sace Dalibin Jami’ar Tarayya Birnin Kebbi
  • Ku Kyautata Rayuwar Jama’a Ba Kan Kanku Ba — Buhari Ga Gwamnonin APC
  • Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Bayan Kashe Ɗan Bindiga A Katsina