Gwamnan Zamfara Ya Yi Jajen Rasuwar Dan Majalisa Aminu K/Daji
Published: 10th, April 2025 GMT
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu.
Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in Kauran Namoda.
“A madadin gwamnatin jiha,muna miƙa saƙon ta’aziyyar mu ga shugaban Majalisar Dokokin, sauran shugabanni a Majalisar, iyalai da al’ummar Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda ta Kudu.
“Muna kuma yin addu’a Allah ƙara ma iyalai jimirin jure wannan rashi. Muna kuma addu’ar Allah gafarta wa marigayin kurakuran sa.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar kwalekwale a Kogin Neja
Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja.
Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan.
Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke ɗauke da fasinjoji da kuma buhunan shinkafa kimanin 200 daga ƙauyen Bugge na Jihar Kogi a zuwa ƙauyen Sokun na Jihar Neja a ranar Laraba da dare.
Wani mazaunin yankin, Baba Alhassan, ya shaida wa wakilinmu cewa, ba a kai ga tantance ainihin yawan fasinjojin da ke cikin kwalwkwalen a lokacin da lamarin ya faru ba, amma an yi asarar duk buhunan shinkafar a hastarin.
NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan NajeriyaYa bayyana cewa daga cikin mamatan har da wani mai sana’ar POS da ƙaninsa ’yan asalin ƙauyen Alaba da ke Ƙaramar Hukumar Lapai
Daraktan Hukumar ba da Agajin Gaggawa na Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da aikin ceto da ƙoƙarin gano ainihin musabbabin hatsarin da kuma irin asarar da ta haifar.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, “Sufurin ruwa shi ne kaɗai hanyar da ta rage da muke amfani da ita domin kai kayanmu kasuwanni saboda hanyar ta yi mummunan lalacewa.”
Wata ’yar kasuwa a yankin mai suna Fatima Muhammad, ta bayyana cewa, saboda nisan tafiyar, fasinjoji sukan yi tafiyar dare domin su isa kasuwa washegari da safe.
Fatima ta ce, “Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne sufuri. Da kwalekwale muka dogara wajen kai kayanmu kasuwa. Wani lokaci kwalekwalen na ɗaukar lodi fiye da kima. Sai ka ga kwalekwale mai ƙarfin ɗaukar mutane 100 ya kwashi sama da haka. Amma ban ga laifin fasinjojin ba, musamman masu son su isa da wuri.”
Jama’ar yankin sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Neja da ta Tarayya da su samar da wadatattun rigunan kariya da jiragen ruwa na zamani sannan su aiwatar da tsauraran hukunci kan masu karya doka.