Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-12@21:31:54 GMT

Man City ta nace wa Guimaraes, Chelsea na son Rodrygo

Published: 10th, April 2025 GMT

Man City ta nace wa Guimaraes, Chelsea na son Rodrygo

Manchester City na nace kan buƙatar ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 27, yayin da take shirin rabuwa da ɗanwasanta na Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33. (UOL esporte – in Portuguese)

Chelsea a shirye take ta biya fam miliyan 102 kan ɗanwasan Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24.

 (Fichajes – in Spanish)

Manchester City na nazarin taya ɗanwasan tsakiya na AC Milan da Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 26, kan tsakanin fam miliyan 42 zuwa fam miliyan 51 duk da ya sabunta kwangilar shi har zuwa 2030. (Calciomercato – in Italian)

Ana sa ran Everton za ta rasa ɗanwasan bayanta na Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 22, yayin da Manchester United da Tottenham ke hamayya kan ɗanwasan. (Sun)

Chelsea da Newcastle na son ɗauko ɗanwasan Benfica da Girka Vangelis Pavlidis, mai shekara 26, kan fam miliyan 85 amma suna fuskantar hamayya daga Barcelona da Atletico Madrid. (Record – in Portuguese)

Arsenal da Liverpool na neman wani zaɓi maimakon Alexander Isak yayin da Newcastle ta dage cewa ba za ta sayar da ɗanwasan na gaba ba. (i paper)

Newcastle da Wolves da Brentford na hamayya kan golan Angers da Ivory Coast Yahia Fofana, mai shekara 24. (Football Insider)

Chelsea na kan gaba wajen buƙatar ɗanwasan tsakiya na Sunderland da Ingila Jobe Bellingham, mai shekara 19, duk da Manchester United da Arsenal da Tottenham da Brighton da Crystal Palace na ribibinsa. (Caught Offside)

Juventus za ta sayar da ɗanwasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, mai shekara 26, a bazara amma tana son kusan fam miliyan 34. (Tuttosport – in Italian)

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Wasanni ɗanwasan tsakiya na mai shekara fam miliyan

এছাড়াও পড়ুন:

NIMASA Za Ta Adana Wa Nijeriya Dala Biliyan 400 A Shekara Daga Cazar Kudaden Safarar Kaya

A cewarsa, wadannan kudaden sun hada da biyan kudaden samar da kariya da na inshore da kuma sauran kudaden da ake biyan kamfanonin na waje.

Ya sanar da cewa, wadanan kudaden da ake biya, na shafar ci gaban tattalun arzikin kasar, inda ya yi nuni da cewa, duk Jirgin ruwa daya da ya yi dakon Danyen Mai ana biyan dala miliyan 130, inda kuma ake cazar kudin da suka kai akalla dala 445,000.

Kazalika, Osagie ya bayyana cewa, ana jigilar Kwantaina kuma ana biyan dala miliyan $150, wanda kuma ake cazar dala 525,000, kan kowacce jigila daya.

Kamfanin Maersk, daya daga cikin manyan kamfanoni a duniya da ke dakon kaya, ya kirkiro kowacce Kwantaina na biyan dala 450, wanda kuma yake cazar daga dala 40 zuwa dala 50 a kan Kwantaina 20.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Newcastle Na Gab Da Samun Gurbi A Gasar Zakarun Turai
  • Jama’ar Gabon sun kada kuri’a a zaben shugaban kasa, na farko bayan mulkin zuri’ar Bongo
  • An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato
  • NIMASA Za Ta Adana Wa Nijeriya Dala Biliyan 400 A Shekara Daga Cazar Kudaden Safarar Kaya
  • Amurka Ta Sayi Kayayyakin Nijeriya Na Dala Miliyan 643 A Wata 2 – Rahoto
  • Yadda Bankin Stanbic IBTC Ke Bunkasa Tattalin Arzikin Abokan Huldarsa
  • Uwargidan Shugaban Kasa Ta Ba Matan Arewa Ta Gabas Su Dubu Tallafin Naira Miliyan 50
  • Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki a NUPRC — Buba Galadima
  • Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki NUPRC — Buba Galadima