ECOWAS ta damu da takun-tsaka tsakanin Aljeriya da Mali
Published: 10th, April 2025 GMT
Kungiyar ci gaban kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ta nuna damuwa kan takun-tsakar da ya kunno kai tsakanin kasar Mali da makwafciyarta Aljeriya, lamarin da ya kai ga kasashen biyu janye jakadu a tsakaninsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ecowas ta ce “Tana bibiyar abin da ke faruwa wanda ya shafi dangantakar da ke tsakanin kasar Mali da kuma Aljeriya.
Ecowas din ta ce ta damu matuka kan lamarin, tana kuma mai kira ga kasashen na Mali da Aljeriya da su kai zuciya nesa, su yi amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen warware sabanin ra’ayin da ke a tsakaninsu.”
Dangantaka tsakanin Mali da Aljeriya, ta yi tsami ne bayan da a makon da ya gabata Aljeriya ta kakkabo wani jirgi maras matuki mallakin sojojin kasar Mali, wanda ta ce ya keta iyakar kasarta.
Mali ta mayar da martani ta hanyar yi wa jakadanta da ke Aljeriya kiranye, haka nan ma kasashen kumgiyar yankin Sahel na AES, sun bi sahun Mali ta hanyar daukar irin wannan mataki, Lamarin da ya sanya ita ma Aljeriya ta mayar da martini makamancin wannan ga kasashen.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Namibiya ta janye bizar shiga ga wasu manyan kasashe na duniya
Namibiya ta janye bayar da biza ga Amurka, Burtaniya, da wasu kasashe sama da 30.
Matakin, wanda majalisar ministocin Namibiya ta yanke tun a watan Yuli, ya fara aiki ne a ranar 1 ga Afrilu.
Ya zuwa yanzu, galibin kasashen Turai, ciki har da Jamus, babbar tushen yawon bude ido a Namibiya, sun ci gajiyar shigowa kasar ba tare da biza ba.
Sabuwar shugabar Namibiya da aka rantsar, Netumbo Nandi-Ndaitwah, tana ci gaba da shirye-shiryen soke bizar shiga kasar ga wasu Karin kasashe, ta yadda ‘yan kasashen za su iya shiga Namibia ba tare da biz aba.
Manufar hakan dai ita ce kafafa harkokin kasuwanci da yawon bude ido a kasar ga yan kasashen ketare, da kuma karfafa kawance da sauran kasashe.