Sudan ta kai karar Hadaddiyar Daular Larabawa a Kotun ICJ
Published: 10th, April 2025 GMT
Jakadan Sudan a Tehran, Abdul Aziz Hassan Saleh, ya tabbatar da cewa, za a gudanar da zaman farko na kotun kasa da kasa da ke birnin Hague a yau Alhamis, domin duba korafin da Sudan ta shigar kan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kan rawar da take takawa a yakin da ake ci gaba da yi a kasar, da kuma goyon bayan da take baiwa mayakan sa kai na Rapid Support Forces, tana mai kallonta a matsayin wani bangare na haddasa rikicin da ke faruwa a Sudan.
A wani taron manema labarai da ya gudanar a wannan Laraba 9 ga watan Afrilu a ofishin jakadancin Sudan da ke Tehran, jakadan Sudan ya yi tsokaci kan laifukan da dakarun RSF suka aikata a jihar Khartoum, inda ya jaddada faruwar munanan laifuka kan fararen hula, da suka hada da kama mutane ba bisa ka’ida ba, da take hakkin fursunoni, da amfani da yunwa a matsayin makami, da kuma cin zarafin mata.
Jakadan ya yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu sojojin Sudan sun kubutar da fursunoni kusan 4,700 da aka sace daga gidajensu, an tsare su ne cikin yanayi na rashin mutuntaka, inda gidajen yari ba su da ko da abubuwan more rayuwa.
Ya kara da cewa, “Rundunar RSF ba su bi ka’idojin shari’a ba wajen mu’amala da fursunoni, a maimakon haka, sun aikata munanan laifuka, har ma a kan kananan yara, ta hanyar yin garkuwa da su tilasta musu ficewa daga gidajensu har ma da karbar kudi daga hannunsu.
Ya kuma yi bayanin cewa har yanzu sojojin Sudan ba su samu damar shiga dukkan wuraren da dakarun RSF ke rike da fararen hula ba, inda ya ce an sace mata da ‘yan mata akalla 200 tare da kai su wuraren da ba a sani ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mahaifi ya yi wa ’yarsa ciki a Bauchi
’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin ya ɗirka wa ’yar cikinsa mai shekara 17 ciki a yankin Kariya da ke Ƙaramar Hukumar Ganjiwa a Jihar Bauchi.
Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya ce an kama mutumin mai shekaru 50 ne bayan samun ƙara cewa ya yi wa ’yar tasa fyaɗe fiye da sau ɗaya a ɗakinsa.
Wakil ya ce a yayin bincike magidancin ya amsa cewa ya sha zakke wa ’yar tasa a gida, kuma bayan an yi mata gwaji a asibiti aka tabbatar cewa tana ɗauke da ciki wata uku.
Ya ce yarinyar ta shaida wa masu bincike cewa a lokacin da mahaifiyarta ta yi tafiya zuwa garin iyayenta a Ƙaramar Hukumar Ningi da ke jihar ne mahaifin nata ya yi amfani da damar ya riƙa lalata da ita.
An kashe mutum kan zargin satar kare a Bauchi Darasi daga rayuwar Dakta Idris AbdulAzeez Dutsen Tanshi ’Yan bindiga sun harbi alkali da ɗansa, sun sace mutane 13 a KatsinaBayan dawowar mahaifiyar ce ta lura da alamun juna biyu a tare da ’yar, kuma bayan ta titsiye ta, ta shaida mata cewa mahaifinta ne ya yi mata cikin.
Wakil ya ce rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.