Jami’an Amurka da na Saudiyya sun tattauna batutuwan da suka shafi Gaza da yankin
Published: 10th, April 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Tommy Bruce a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa: Ministocin harkokin wajen Amurka da na Saudiyya sun tattauna kan yunkurin diflomasiyya a Gaza na sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma samar da tsagaita bude wuta mai dorewa a Gaza inda Hamas ta samu cikaken kwance damarar makamai da nakasassu.
An gudanar da taron ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yin kiraye-kirayen a samar da mafita a siyasance a yakin Gaza, inda Isra’ila ta kashe Falasdinawa fararen hula fiye da 50,000 tun daga watan Oktoban 2023 (Bahan 1401).
A yayin da Amurka ke ci gaba da goyon bayan munanan hare-hare na gwamnatin sahyoniyawan da kuma kokarin shiga tsakani kan yarjejeniyar daidaita alaka tsakanin Saudiyya da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, Riyadh ta jaddada tsagaita bude wuta nan take a zirin Gaza da kuma hanyar samar da kasashe biyu.
A watan da ya gabata, shugaban Amurka Donald Trump ya ce watakila ya ziyarci Saudiyya tun a farkon wannan watan (Afrilu). A wa’adin farko na gwamnatin Trump a shekarar 2017, Saudiyya ita ce kasar farko da Trump ya fara zuwa kasashen waje. Duk da haka, Axios ya ruwaito cewa tafiya za ta faru a tsakiyar watan Mayu.
Ministocin harkokin wajen Amurka da na Saudiyya sun kuma tattauna kan wasu batutuwan yankin da suka hada da yakin Sudan da Yemen.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce: Ministocin harkokin wajen Amurka da na Saudiyya sun kuma amince da cewa, sojojin kasar Sudan da dakarun da ke ba da goyon baya cikin gaggawa su koma kan teburin sulhu, da kare fararen hula, da bude kofofin jin kai, da kuma komawa ga farar hula.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Amurka da na Saudiyya sun harkokin wajen Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
A Yau Asabar Ne Ake Bude Tattaunawa A Kasar Oman Akan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
Tun da safiyar yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya isa birnin Mascut na kasar Oman da can ne za a yi tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba a tsakanin jamhuriyar musulunci da Amurka.
Jim kadan bayan isar tasa birnin Mascut ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya gana da mai masaukinsa Sayyid Badar al-Busa’idi,inda ya mika masa takardu akan mahangar Iran.
A yayin ganawar da bangarorin biyu su ka yi, ministan harkokin wajen Iran ya yaba da matsayar Oman akan batutuwa da dama su ka shafi wannan yankin na yammacin Asiya.
Daga cikin masu yi wa ministan harkokin wajen na Iran rakiya da akwai mataimakinsa a fagen dokokin kasa da kasa Kazim Garib Abadi, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ambata.
Da marecen yau bayan la’asar ne dai za a yi tattaunawar ta Oman.
Iran da Amurka za su yi tattaunawa ne ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman ba ta gaba da gaba.